AWWALUN DAUDAWA YA TUBA YA MIKA KANSA

0
196

AWWALUN DAUDAWA YA TUBA YA MIKA KANSA
@ jaridar taskar labarai
Jigon Wanda ya jagoranci satar daliban makarantar sakandaren kankara ta jahar katsina ya tuba ya kuma mika kansa ga hukuma.
Awwalun daudawa ya mika kansa tare da yaransa da kuma bayar da wasu makaman dake wajen sa bindiga AK 47 guda 20.RPG guda daya.PKT guda daya.aljifun harsasai guda ashirin.sai harsasai guda 72.makaman an ba gwamnan zamfara, shi kuma ya mika su ga kwamishinan yan sanda na jahar zamfara.
Awwalun daudawa ya kai kansa ga hukumomin gwamnatin jahar zamfara Wanda dama yana a wani daji ne cikin yankin na zamfara.
Awwalun daudawa ya tabbatar wa da wani babban jami in gwamnatin katsina cewa ya tuba don Allah Dan ya zama mutumin kirki.ba don komai ba.
Awwalun daudawa yana zaune a dajin gidan jaja dake jahar zamfara kuma dabar shi itace ta hana duk garuruwan katsina iyaka da jibia zuwa kankara zaman lafiya.
Su suka hana hanyar katsina zuwa zamfara sakat. Lokacin mika kansa da makamansu ya jinjina ma gwamnan zamfara dakta Bello matawalle ya kuma ce ya amshi kiranshi na a zauna lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here