GARIN RANDAGI NA GAB DA ZAMA KUFAYI SABODA MAHARA ‘YAN FASHIN DAJI

0

GARIN RANDAGI NA GAB DA ZAMA KUFAYI SABODA MAHARA ‘YAN FASHIN DAJI

Daga Auwal Adam

Randagi Gari ne wanda yake a yammacin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jahar kaduna. Gari ne mai girman gaske mai fadin kasa ta ko wane bangare, domin masu iya kididdiga sun tabbatar da cewa garin zai iya zama karamar hukuma mai cin gashin kansa.

Amma yau barayi sun taso garin gaba kusan kullum sai sun shiga cikin garin sunyi ta’addanci, sun mai da garin wajen yin dabdala so, duk lokacin da ran su yake so zasu shiga garin suyi abinda sukeso ba tare da jin shakkan kowa ba.

Yanzu dai mazauna garin da yawan su tuni sun tattara kayan su sun bar garin, musamman kauyukan dake a gefen garin, wasu tuni suka dawo cikin garin Birnin-Gwari, wasu kuma suka nufi Niger domin tseratar da rayuwar su.

Wannan ba qaramin tashin hankali bane ace rana tsaka mutum yabar asalin garin shi yana ji yana gani, kuma ba tare da an dauki wani kwakkwaran mataki ba.

Muna Kira ga shuwagabanni da suji tsoron Allah su waiwayi wadannan bayin Allahn.
Ya ku shuwagabanni ga inda ya kamata ku maido da hankalin ku nan, ba wai maganar sabunta katin zabe ba.

See also  HARE HARE A SABUWA DA FASKARI Muazu hassan

Wannan ke nuna cewa baku dauki rayukan Al’umma da muhimmanci ba, ana kashe Al’umma ana koran su daga matsugunnin su amma ku hankalin ku ya karkatu wani waje daban.

Ina fadin wannan ne ba tare da wata manufa ba sai don tunatar da wadanda alhakin ya ratayu a wuyan su, duk da nasan akwai wadanda basu son ganin irin wannan rubutun, na sani akwai wadanda ji suke kamar su kashe ni saboda tsabagen jin bakin ciki, to babu yadda kuka iya. Fatan mu dai shine a samu mafita.

Yaa ubangija mun tuba kai kadai ne wanda zai iya magance mana wannan matsalar, wadanda suka ce sune zasu magance matsalar suma ya tabbata sun gaza ba zasu iya ba, yaa Allah ka tausaya musu ka kawo musu mafita ta Alheri.
Mun dauko daga shafin jaridar Al mizan na Facebook..bamu cire komai ba .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here