KADDAMAR DA AIKIN JIRGI DAGA KATSINA

0

KADDAMAR DA AIKIN JIRGI DAGA KATSINA
daga shafin Abdulhadi bawa
Ss social media

CIkin iko da yardar Allah ga mu a Kwarin Tama dake kan hanyar zuwa Army Barrack daga Shinkafa domin muhimmin buki aza harsashin gina layin dogo (hanyar jirgin kasa), wadda za ta hada Kano, Katsina, Jibia da Maradi ta Jamhuriyyar Nijar. Haka kuma da wadda za ta hada garin Dutsen Jihar Jigawa.

Baya ga Gwamna Aminu Bello Masari Mai masaukin baki, akwai Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa da kuma Gwamna Zakari Oumarou na jihar Maradi.

Akwai Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu, Alhaji Tasi’u Maigari Zango Shugaban Majalisar Dokoki ta jiha, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa Sakataren Gwamnatin jihar Katsina.

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi wanda a karkashin Ma’aikar shi ne wannan aiki zai gudana.

Masumartaba Sarakunan Katsina, Kano da Dutse, Alhaji AbdulMumin Kabir Usman, Alhaji Aminu Ado Bayero da Alhaji Muhammadu Sanusi da kuma wakilin Maimartaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouq Umar duk suna wannan wuri.

Akwai Ministoci da Wakilan Majalisun Dokoki dana zartaswa na jihohin Katsina, Kano da Jigawa.

Addu’ar mu Allah Yasa a fara lafiya kuma a gama lafiya. Allah Yasa al’ummar mu suci gajiyar wannan aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here