MU ƘADIRAWA MUNA TARE DA SHEKIH ABDULJABBAR NASIRU KABARA HAR GOBE–Bazallahi
Daga Shekih Bazallahi Nasiru Kabara
Malamin Addinin muslinci A Nigeria Kuma Kani Ga Dr Qariballahi Nasiru Kabara Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Dan Uwansa Dr Abduljabbar Nasiru Kabara
Jaridar Kakaki ta rawaito Shekih Bazallahi na Bayyana Cewa Mutukar Gwamnati Da Gaske Takeyi Wajen Kawo Gyara A Bangaren Addini A Jihar Kano Tofa Sai Dai Ta Tursasawa Kowanne Malami Karantarwa Da Mazahabar Malikiyya Kamar Yadda Ya Faru A Kasar Marocco Da Kasar Saudiyya Domin Hakanne Kawai Zai Samar Da Daidaito
Amma Bazai Yiwu A Kyale Wani Malami Yana Kafirta Iyayen Annabi (SAW) ba
A Cikin Garin Kano Ake Karantar Da Wannan Fahimta Ta Kafirta Iyayen Annabi (SAW) Ana Cewa Kafirai Ne’Yan Wuta Wa’iyazubillah
A Garin Kano Ake Karanta Allahntar Da Wani Shehi Tare Da Yi Masa Wakoki Na Shirka Kuma Kowa Yanaji
A Garin Kano Wasu Malamai Suke Karantar Da Cewa Allah Yana Sama Kuma Yana Da Hannu Yana Da Kafa
Duk Wadannan Mutane Suna Garin Kano Suna Cigaba Da Karantar Da Aqidunsu Ba Tare Da Tsangwama Koh Zagi Ba
Amma A Haka Suka Hade Kai Wajen Ganin Sun Yaki Dan Uwanmu Mlm Abduljabbar Nasiru Kabara Suna Yi Masa Kazafin Cewa Wai Yana Zagin Annabi (SAW) Da Sahabbai
Kuma Ina Rantsuwa Da Allah Cewa Jinin Shekih Nasiru Kabara Bazai Taba Zagin Manzon Allah (SAW) ba Suma Masu Yi Masa Qage Sun Sani Cewa Mlm Abduljabbar Ba Zagin Annabi Ko Sahabbai Yakeyi Ba
Gidan Shekih Nasiru Kabara Ba’a Koyar Da Komai Sai Soyayyar Manzon Allah (SAW) Kuma Har Yanzu Shekih Abduljabbar Yana Kan Wannan Tafarki
Bamu Da Burin Da Yafi Kullum Muga An Sasanta Rikicin Da Yake Faruwa A Tsakanin’Ya’yan Malam Nasiru Kabara Wannan Shine Fatan kowanne bakadire Masoyin malam nasiru kabara na gaskiya
Saboda haka zamu kira taro na gaggawa zamu zauna da sheikh kariballahi nasiru Kabara da sauran ‘ya’yan Malam Zamu Gayawa Halifa Gaskiyar Abinda Yake Faruwa domin nasan magauta basa fada masa gaskiya shiyasa har yake goyon bayan matakin da gwamnatin Kano ta dauka na dakatar da karatun malam abduljabbar
Yan izala ba masoyanmu bane da har zamu hada kai dasu mu yaki dan uwanmu na jini.