Yawan masu zaɓe a Nijeriya ya tsaya tsakanin kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari, inji INEC

0

Yawan masu zaɓe a Nijeriya ya tsaya tsakanin kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari, inji INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa yawan masu zaɓe a Nijeriya bai fi kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari na waɗanda su ka yi rajista a zagaye biyu na zaɓuɓɓukan da aka yi na baya-bayan nan ba.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron tuntuɓa na farko da hukumar ta shirya tare da ƙungiyoyi masu zaman kan su (CSOs) na shekarar 2021 wanda aka yi a ranar Talata a Abuja.

Yakubu ya ce a yayin da wasu zaɓuɓɓukan sun fi samu yawan fitowar masu zaɓe, a wasu kuma ba a samu fitowar mutane sosai ba.

Ya ce, “A lokutan zagaye biyu na zaɓe da aka yi na baya-bayan nan, ciki har da zaɓuɓɓukan da aka yi ba a lokutan da aka saba yin zaɓe ba, fitowar masu zaɓe don kaɗa ƙuri’un su a sassan ƙasar nan ya tsaya ne tsakanin kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari.

“A yayin da a wasu zaɓuɓɓukan an fi samun fitowar masu zaɓe fiye da wasu, wasu zaɓuɓɓukan cike gurbi da aka yi a watannin baya sun samu ƙarancin masu fitowa don su kaɗa ƙuri’un su da wajen kashi 8.3 cikin ɗari a mazaɓun da ke cikin birane waɗanda ke da masu zaɓe da su ka yi rajista da su ka kai sama da miliyan 1.2 a birnin da ya fi kowanne cinkoson yawan jama’a.

“Wannan ba abin daɗi ba ne idan an kwatanta shi da yadda masu zaɓe kan fito aƙalla kashi 65-70 cikin ɗari a wasu ƙasashen, har ma a yankin Afrika ta Yamma.”

Shugaban na INEC ya ce gaskiya ne ƙungiyoyi masu zaman kan su sun sha yin kira ga hukumar da ta nemo hanyoyin magance matsalar.

Yakubu ya ce a matsayin su na masu sa ido kan harkokin zaɓe da aka amince da su, wasu daga cikin ƙungiyoyin sun miƙa wa hukumar rahotanni, ya na mai ƙarawa da cewa bayan hukumar ta yi wa rahotannin kyakkyawan nazari, sai ta fahimta sosai cewa sun damu ne da yadda ake samun raguwar masu fitowa su yi zaɓe a Nijeriya.

Ya ce, “Hukumar ta yi tunani sosai kan wannan al’amari. Shawarar da mu ka yanke ita ce akwai dalilai da yawa da su ka jawo raguwar masu kaɗa ƙuri’a.

“Daga cikin su akwai rashin isasshen ilimantar da masu zaɓe da haƙƙoƙin su, da rashin ingancin gangamin jama’a, da tsoron ɓarkewar rikici a lokacin zaɓe, da rashin cika alƙawarin da zaɓaɓɓun shugabanni su ka yi a lokacin takara, da kuma rashin yardar da jama’a ke yi wa hukumomin gwamnati.

“A yayin da Hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da ƙungiyoyi masu zaman kan su da ma dukkan masu ruwa da tsaki don tunkarar waɗannan matsalolin, mun kuma yi amanna da cewar samun ƙarin rumfunan zaɓe wani abu ne muhimmi wajen fitowar masu zaɓe a lokacin zaɓuɓɓuka.

“Ƙasashe masu yawan mutane da ke fitowa domin kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuɓɓuka kuma su na da isassun wuraren kaɗa ƙuri’a cikin sauƙi da aka tanadar domin masu zaɓe da ke da rajista waɗanda a kan yi wa sauyi lokaci-lokaci saboda ƙaruwar yawan masu zaɓe, to amma abin baƙin cikin shi ne mu ba haka abin ya ke ba a Nijeriya.”

Yakubu ya yi nuni da cewa Nijeriya ta na da rumfunan zaɓe guda 119,973 waɗanda aka samar a cikin 1996 a ƙarƙashin tsohuwar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, wato NECON, domin masu zaɓe da aka ƙiyasta yawan su ya kai miliyan 50.

“Har yanzu ba a ƙara yawan su ba a shekaru 25 da su ka gabata duk da yake yawan masu zaɓe da su ka yi rajista sun ƙaru zuwa 84,004,084 ya zuwa 2019. Kuma yawan zai ƙaru bayan mun ci gaba da yi wa sababbin masu zaɓe rajista saboda Babban Zaɓen 2023.”

Ya ce INEC ta yi nazarin dukkan ƙoƙarin da aka sha yi a baya da nufin faɗaɗa wuraren kaɗa ƙuri’a, wato a ƙara rumfunan zaɓe, a shekarun 2007, 2014 da kuma kafin Babban Zaɓen 2019 da dalilin da ya hana a cimma nasarar hakan.

Yakubu ya ce hukumar ta gama fahimtar cewa akwai yiwuwar ba ta isar da burin ta ga sauran ‘yan Nijeriya ba domin a samu shawarwarin su, don haka ba a fahimci abin ba har aka siyasantar da shi.

Ya ce zaman da INEC ta yi da waɗannan ƙungiyoyi masu kan su an yi shi ne a matsayin ci gaba da tuntuɓar da ake yi da dukkan masu ruwa da tsaki, tare da fatan ta hanyar yin hakan hukumar za ta fi isar da ƙudirin ta ga ‘yan Nijeriya.

To amma ya yi kira ga kowa da kowa da ya kawo nasa shawarwarin domin a magance matsalar ba tare da ɓata lokaci ba da kuma fatan za a fito da hanyar da za a bi a riƙa yi wa tsarin kwaskwarima a nan gaba idan buƙatar hakan ta taso.

Yakubu ya ce, “Na tabbatar da cewa ta hanyar yin aiki tare, za mu kafa tarihi wajen ganin a ƙarshe mun magance wannan matsala da ta shafe shekara 25 ta bai wa masu zaɓe damar samun ƙarin rumfunan zaɓe a Nijeriya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here