Aika-aika ne tsantsa yunkurin Gwamnatin Kano na rushe gadar kofar Nasarawa- ja’afar Sani Bello
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Ɗan siyasar nan da ya nemi jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen shekara 2015 Jafar Sani Bello ya bayyana ƙudurin gwamnatin jihar Kano na rushe gadar sama ta ƙofar Nasarawa a matsayin aika – aika kuma awon igiya.
Jafar Sani Bello wanda ya yi shuhura wajen bayyana raayinsa a fili ba tare da tsoro ba, musamman a gwamnatin Muhammad Buhari,
Ja’afar ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook a matsayin martani ga shirin gwamnatin jihar Kano na rushe gadar saman.
Ya kara da cewa “Rushe gadar Kofar Nassarawa Yanzu aika-aika ne, awon Igiya” In ji Jafar Sani Bello
Wannan dai yana zuwa ne a dai-dai lokacin da al’ummar jihar Kano ke bayyana ra’ayoyinsu akan bayanan da kwamishinan yada labarai cewa zaa rushe gasar a sake wata sabuwa saboda rashin inganci.