KUNGIYAR MANOMA TA KASA (AFAN) TA DUKUFA DOMIN BUNKASA NOMAN RANI

0

KUNGIYAR MANOMA TA KASA (AFAN) TA DUKUFA DOMIN BUNKASA NOMAN RANI

Dahiru Muhammad Maihula

Shugaban kungiyar Alh. Farouk Rabiu Mudi ya bayyana wannan yunkurin nasu ne awata ziyarar gani da ido a karamar hukumar Kabo, da Gwarzo da kunchi, yayin wata ganawa da manema labarai. Farouk Mudi ya bayyana cewa yinkurin domin bunkasa noman rani a duk fadin kasa da abinci musamman kasar ta ci da kanta batareda ta dogara da na kasashen ketare ba.

Shugaban Farouk Mudi yacigaba da cewa Allah ya albarkace wannan yanki da ruwa da dam dam da kasar noma tunda muna da wannan akwai bukatar adinga anfani da dam dam domin noman rani, yinhakan zai bawa shine manomi zai inganta sanaartasa domin samun arzuki

Haka zalika yasake kira da masu kudinmu da su cigaba da saka kudade domin bunkasa noma a fadin kasa tayin anfani da dam dam na ruwa zai taimakama rage anbaliyar ruwa na dam dam din da muke dasu a noman Rani
su kansu manoma da suke tafiya cirani idan da wannan tsarin na noman rani bazasuje ko nan da chanba, wannan barna da ruwa yakeyi na anbaliya zaa sami sauki, Farouk Rabiu mudi yacigaba da cewa, nadaya idan akai anfani da wannan ruwan barna zata dakata, nabiyu sakardashi ruwan jama’ar manoma zasuyi anfani dashi ta susami arzuki kuma gwamnati tasami kudin shiga ta wannan wannan shine da lilin da yasa mukaga cewa yakamata muzo wannan wuri.

Sannan mukai tunanin cewar mufara shigo da manyan manoma da masu da masu kudi domin shigowarsu su saka hannun jari a wannan harkata noma domin noma kasuwanci ne kamar yanda kowanne kasuwanci yake, duk sanda manomi zai dauka saidai a tallafa masa daganan yasan saidai ya kare a tallafawa. Idan aka fito da wannan tsari na noma zai rage tsadar noma da muke dashi arufe border ko abude border duk baitaso ba.

Wannan tsarin gwamnati da race ayi shine babbar gudunmawarta cewa ayi shine babban aiki kuma munsami sahalewarta, takuma ba da ruwanta tabawa al’ummarta sukuma manoma sunbada filayensu mukuma shugabanni manoma mune a tsakanin da gwamnati da manoma idan akai wannan hanya ta noma inda gwamnati takeda nata misali idan akaje kura kaga anabiyan kudin ruwa na hadeja jama’are da ake biya wannan malamin yasa kudinsa ta nan zaisamu.

Yabada misali inda yakecwa kamar wanda akabawa wutar lantarki KEDCO da aka siyarwa su ke bi gida Gida abada kudin wuta wannan ma haka tsarin yake toh amma duk manomi zaiga wannan sauki, nafarko dai manomi zai sayi inji akalla 40,000 kadinga zuba mai duk sati kadinga zuba mai agonarka stsari. watakila kabiya kudin da kudin da kakekashe a sati 4. Shikuma wannan kudin da ake rainawa anan zaimaida kudinsa, sannan kaikuma ribarka ta karu sannan kuma abincin ya saukko don nomanka yazo da araha bakada sayen inji.

A tambayar da mukaiwa wasu manoman sun nuna farin cikin su dangane da wannan tsari Mal. Usman Nadada shu’aibu dake garin gudi a karamar hukumar Kabo ya ce yana noma timatiri, albasa dakuma masara ya bayyana cewa indai wannan tsari ya dore toh kakarsa ta yankesaka.

Haka zalika Mal. Sunusi Alhasan Shine Shugaban kungiyar manoma na karamar hukumar gwarzo ya ce lokacin da shugaban kungiyar manoma ta kasa Farouk Rabiu Mudi yazo masu da wannan albishir da cewa akwai wani bawan Allah zaizo yayisu wannan hanyar ruwan (channels) daga dam dam wallahi sainaji abin kamar daga sama nakwana da abin

Sunusi Alhasan yacigaba da cewa gari yawaye yaje yasami masu unguwannin da manoma nayi masu wannan bayani da sanardasu, gaskiya muna nuna godiyarmu ga shi wannan bawan Allah da ya kawo mana wannan cigaba Allah sakamasa da alheri idan iyayensa sunrasu Allah yajikansu. Anan yanzu muna noma kadada dari saboda injinan da zakazo kana sayen mai na fetir amman zuwan wannan tsari munada fiyeda kadada dubu uku da bama iya noma kuma jama’armu saidai su tafi cirani idan akasami wannan tsari toh kuwa fiyeda haka ma zamu noma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here