Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint ya sabunta rajistar sa a APC

0

Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint ya sabunta rajistar sa a APC

Shugaban kamfanin buga jaridun Manhaja da Blueprint, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya sabunta rajistar sa ta zama ɗan jam’iyyar APC a rumfar zaɓen sa da ke Malagi, a Ƙaramar Hukumar Gbako da ke Jihar Neja.

Bayan ya kammala rajistar tasa a ranar Juma’a, Alhaji Idris ya yaba da yadda aikin yin rajistar ke gudana cikin lumana a rumfar zaɓen su, sannan ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC a faɗin jihar da kowa ya tabbatar da ya yi rajista ko sabunta rajistar sa.

Ya ce, “Na yi matuƙar farin ciki da yadda aikin yin rajistar ke gudana. Wannan wata alama ce mai nuna yadda ‘yan jam’iyyar da ma masu sha’awar shigar ta ke da burin bunƙasa jam’iyyar da ma dimukraɗiyya a jihar.

“Don haka na ke kira ga ɗaukacin ‘ya’yan jam’iyyar da ma masu sha’awar su shige ta a jihar da kowa ya je ya yi rajista.”

Alhaji Idris, wanda har wa yau shi ne shugaban kamfanin Bifocal Group da gidan rediyon WeFM da ke Abuja, ya ce ya yi koyi ne da Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani-Bello da dukkan shugabannin APC na ciki da wajen Neja, waɗanda su ka riga su ka yi tasu rajistar a wurare daban-daban, wajen sabunta rajistar sa.

See also  Gwamna Aminu Waziri Tambuwal tare da mawakan darikar Kwankwasiyya

Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihar da su riƙa shiga ana damawa da su a harkoki a matakin jiha da ƙasa maimakon su zama ‘yan kallo.

A cewar sa, “Wajibi ne mu haɗa hannu wajen ciyar da tsarin dimukraɗiyy a Nijeriya gaba, mu gina al’ummomin mu, jihar mu da ma ƙasa baki ɗaya ta hanyar shiga ana damawa da mu, amma ba mu zama ‘yan a bi yarima a sha kiɗa ba.

Jigon ya yaba wa Shugaba Buhari da kuma Gwamna Bello bisa yadda su ka sakar wa kowa mara don tsofaffi da sababbin ‘yan jam’iyyar kowa ya yi rajistar sa ba tare da wata takura ba.

Daga bisani ya shawarci jama’a da su kiyaye dukkan dokokin yaƙi da korona da aka shimfiɗa yayin yin rajistar domin taimaka wa ƙoƙarin gwamnati wajen yaƙi da cutar.

A ƙarshe, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya yi godiya ga dukkan waɗanda su ka yi masa rakiya zuwa wajen sabunta rajistar sa waɗanda su ka haɗa da shugabannin APC na yankin da abokan hulɗa da magoya bayan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here