Jamiyyar PDP ta bukaci ‘yan sanda su kama shugaban APC na jihar Kano

0

Jam’iyyar PDP ta bukaci babban sifeton yan sanda na kasa Muhammad Adamu da kama tare da gurfanar da shugaban jam’iyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas bisa kalaman tunzura jama’a da yake yi.

Bayanin haka ya fito daga shugaban jam’iyar PDP na jihar Kano Alh. Wada Sagagi ta cikin wata sanawa da jam’iyyar PDP ta fitar a yau Litinin a nan Kano.

Wada Sagagi ya ce tuni suka aike da takarda zuwa ga babban sifeton ‘yan sandan da sauran hukumomin gwamnati domin daukar matakin da ya kamata.

Ya ce ko kadan basu yi mamaki ba don kuwa dabi’ar Abdullahi Abbas ce yin kalaman tunzuri ga magoya bayan su, saboda shi mutum ne mai barin zance.

See also  LIKEN DALOLI A BUKIN GIDAN FARFESA SANI MASHI

“Ya ce duba da yadda Demokradiya take, irin wadannan kalaman ana bukatar a dauki mataki a kansu,” a cewar sa.

Idan za a iya tunawa dai a baya bayan nan ne Abdullahi Abbas ya yi wasu kalamai da jam’iyar adawa ke kallon su a matsayin kalaman tunzuri.

Daga cikin kalaman da suke zarginsa da yi akwai jawabin da ya yi lokacin rantsar da shugabanin kananan hukumomi 44.

“Ku farmaki tare da hukunta duk wanda ya yi yunkurin satar akwati yayin zaben 2023.

“Ku dauki mataki a hannunku kuma ba abinda zai faru.

“Ina kira ga matasan jam’iyarmu da su tanadi makamansu a yanzu don akwai lokacin da za a yi amfani dasu….. Inji Abdullahi Abbas

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here