YAN SANDA SUN SAKE KAMA MAHADI SHEHU

0


muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Yan sanda sun sake kama mahadi shehu a tashar jirgin kasa ta kubwa dake Abuja.kamar yadda wata majiya ta tabbatar ma jaridun mu a hukumar yan sanda
Sun kama shi yau Talata 16/2/2021 da Rana lokacin yana a cikin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna
Yan sanda sun kama shi ne bisa binciken da suke na wata kara da gwamnatin katsina ta shigar akan sa.
Wata majiya tace yan sanda suna son kawo mahadi shehu a kotu nan katsina don gabatar dashi.kafin satin nan ya kare.
Mun yi kokarin jin ta bakin wani na kusa da mahadi shehu amma mun kasa.domin kuwa lambobin da ake samun mahadi duk a kashe suke . Ba kuma Wanda zamu iya tabbatar ko karyata labarin ta bangaren mahadi shehu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here