Gwamnatin Tarayya ta ɗau mutum 5,000 aikin sa ido kan raba kuɗin tallafin ‘N-Power’ da sauran su

0

Gwamnatin Tarayya ta ɗau mutum 5,000 aikin sa ido kan raba kuɗin tallafin ‘N-Power’ da sauran su

Gwamnatin Tarayya ta ɗauki mutum 5,000 da za su yi aikin sa ido kan yadda ake raba biliyoyin naira na agaji ga ‘yan Nijeriya a ƙarƙashin Shirin Tallafin Jama’a, wato ‘National Social Investment Programme’ (NSIP).

Daga cikin wannan yawan, masu sa ido 195 an zaɓo su ne daga Legas.

An fara yi wa ma’aikata ‘yan sa idon atisaye na mako biyu.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ƙirƙiri shirin na NSIP a cikin 2016 da nufin ceto jama’a daga ƙangin fatara da yunwa kuma shirin ya ƙunshi shirye-shirye daban-daban na agaji waɗanda su ka haɗa da shirin samar da aikin yi – irin su ‘NPower’, ‘National Home Grown School Feeding Programme’ (NHGSFP), ‘Conditional Cash Transfer Programme’ (CCT) da ‘Government Enterprise and Empowerment Programme’ (GEEP).

Wasu shirye-shiryen su ne: ‘Tradermoni’, ‘Marketmoni’, ‘Farmermoni’, ‘special grant transfer’, da kuma ‘public workfare and skills for jobs’.

Haka kuma za a ƙaddamar da dunƙulalliyar rajistar jama’ar ƙasa (‘Unified National Social Register’) wadda za ta samar da taskar bayanai na dukkan shirye-shiryen tallafi na gwamnati, wanda ya haɗa da jerin sunayen waɗanda su ka amfana a dukkan faɗin ƙasar nan.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta faɗa a Legas ranar Alhamis cewa mutum 5,000 da aka ɗauka ɗin za su sa ido ne kan masu amfana da shirye-shiryen tallafin a makarantu, gidaje, da wajen kasuwanci da nufin tabbatar da cewa ana cimma burin shirye-shiryen kamar yadda aka tsara.

See also  GUARANTEEING ACCOUNTABILITY IN THE BUHARI ADMINISTRATION'S NATIONAL SOCIAL INVESTMENT PROGRAMMES!

Yayin da ta ke magana ta bakin Mataimakiyar Darakta mai kula da Bincike da Tattara Bayanai, Misis Jumai Ali, Ministar ta ce ayyukan da ke cikin shirye-shiryen su na da yawan gaske, domin sun shafi jama’ar ƙasa da yawan su ya kai miliyan 13 a faɗin jihohi 36 da Yankin Birnin Tarayya (FCT) da za su amfana daga tallafin Gwamnatin Tarayya.

Haka kuma ta bayyana cewa gwamnatin za ta haɗa gwiwa da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, wato EFFC da ICPC, da kuma hukumomin tsaro don duba ma’aikatan sa idon da za su so su aikata ba daidai ba.

A jawabin ta a lokacin bikin ɗaukar ‘yan sa idon na shirin na NSIP, Kwamishinar Samar da Dukiya da Aikin Yi ta Jihar Legas, Misis Yetunde Arobieke, ta ce dukkan shirye-shiryen NSIP sun yi tasiri tare da inganta rayuwar matan karkara kuma sun cire mutane da dama daga cikin fatara.

Ta ce a ƙoƙarin ta na rage rashin aikin yi, gwamnatin su ta kafa Gidauniyar Samar Da Aikin Yi ta Jihar Legas (LSETF).

Kwamishinar, wadda ita ce jami’a mai kula da shirye-shiryen tallafi na NSIP a Jihar Legas, ta ce jama’a sun amfana sosai da agajin kuɗi da kayan aiki da aka ba su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here