ME YA HANA HADIZA BALA USMAN RIJISTA A MUSAWA?

0

ME YA HANA HADIZA BALA USMAN RIJISTA A MUSAWA?

Daga Mu’azu Hassan
@Katsina City News

A makon da ya gabata ne Hajiya Hadiza Bala Usman, Shugabar Hukumar Tashoshin ruwa na Nijeriya ta je hedikwatar jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta sabunta rijistarsa ta zama cikakkiyar ‘yar jam’iyyar APC.

Zuwan ta da sabunta rijistar ya cika shafukan yanar gizo a Katsina, amma kuma ya bar baya da kura.

Duk masu wannan sabuntawar suna yi a ne garinsu a mazabarsu a kuma rumfar da suke jefa kuri’a, kuma ana shirya taro ne sosai duk kafofin sadarwa suna watsa me aka yi.

Sabunta rijistar ta zama kamar kowa yana gwada kwanjin tasirinsa a cikin yankinsa da mazabarsa.

An yi ta shaci-fadi da fadin dalilai marasa tushe na kin zuwan ta Musawa, kuma babu wani bayani da ya fito daga wajen ta, ko na kusa da ita game da abin da ya hana ta zuwa.

Katsina City News mun yi binciken don ji ko mene ne dalili?

Alhaji Bala Abu Musawa, mataimakin Shugaban riko na mataimakin jam’iyyar APC na shiyyar Funtua, ya fada mana cewa, garin Musawa yana cikin jimamin rasuwar mutumin kirki, Alhaji Dikko Abdullahi Inde, shi ne dalilin da ya hana ta zuwa ta yi taron don sabunta rijistarta.

Ya ce; “Mun shirya tsaf domin taryar ta da ba ta katin, sai wannan babban rashi ya faru, kuma ga lokacin sabun ta rijistar yana gaf da wucewa (lokacin ba daga ba cewa an kara mako uku), sai muka yanke shawarar ta karba a hedikwatar APC ta Katsina.

“Daga nan Musawa muka tada motoci suka je can, duk tarbar da ake yi aka yi mata”, in ji shi.

Bala Abu ya kara da cewa; “Da kuma mun san za a kara kwanaki da mun jinkirta, sai an gama zaman makoki da mako biyu nan gaba, sai ta zo nan garin na Musawa, ku ga yadda za mu nuna mata kauna”.

Bala ya kara da cewa; “Hajia Mariatu Bala Usman a nan Musawa ta yi tata rijistar da sauran ‘Yan’uwanta”.

Wannnan shi ne dalilin ba wani abu ba.
________________________________________________
Jaridar katsina city news na bisa yanar gizo www.katsinacitynews.com da sauran shafukan sada zumunta na Facebook, Instagram,Twitter da sauran su.tana tafiya tare da jaridar taskar labarai dake a www.taskarlabarai.com da kuma the links news dake a www.thelinksnews.com. duk sako a aiko ga 08143777779.email.katsinaoffice@ Yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here