SUNAYEN HAUSAWA DA MA’ANONINSU

0

MU SAN HAUSA

SUNAYEN HAUSAWA DA MA’ANONINSU

*TANKO*: Yaron da aka haifa bayan an haifi mata biyu ko fiye.
*KANDE*: Yarinyar da aka haifa bayan an haifi maza biyu ko fiye.
*KILISHI* :Yarinyar da aka haifa kuma a dadai wanna lokacin babanta ya samu arziki ko sarauta.
*BARAU*: Yaron da aka haifa ya rayu, amma an haifa wasu kafin shi ba su rayu ba.
*SAMBO*: Yaron da aka haifa bayan maza da yawa kuma ya Zama Dan autan maza.
*TALLE* :Yaron/yarinya da mahaifiya ta rasu tana gama haihuwarsa/ta.
*AUDI* :Yaron/yarinyar da mahaifi ya rasu kafin a haife shi ko ta.
*MIJIN-YAWA*: Yaron da aka haifa dukkanin kakannin sa suna raye.
*DIKKO*: Yaron da aka fara haifa (Dan fari).
*SHEKARAU*: Yaron da ya shekara a ciki
*MAIWADA*: Yaron da aka haifa iyayensa suna cikin wadata.
*GAMBO*: Yaron/yarinyar da aka haifa bayan tagwaye.
*CINDO*: Yaron/yarinyar da aka haifa da yatsu shida.
*MARKA*: Yarinyar da aka haifa lokacin marka-marka.
*ALHAJI*: Yaron da aka haifa lokacin aikin haji.
*AZUMI* ; Yaron/yarinyar da aka haifa lokacin azumi.
*SARKI*: Yaron da aka sa wa sunan sarkin garinsu.

*SUNAYEN NA’URORIN BATURE DA AKA HAUSANTAR DA SU*

*Ford = Hodi*
*Bedford = Bilhodi*
*Mercedes = Marsandi*
*Peugeot = Fijo*
*Volkswagen = Baksuwaja*
*Volkswagen Beetle = Ladi ba duwawu*
*Fiat = Fet*
*Austin = Ostan-Ostan*
*Bus = Kiya-kiya* (borrowed from Yoruba)
*Station wagon = Dafa-duka*
*1973 Mercedes-Benz W114/W115 = Bagobira*
*1982 Toyota Corolla = Bana ba harka*
*Hatchback/coupe = ‘Yar kumbula*
*Long bus = Safa*
*Ten-wheel = Tangul*
*Mercedes 911 truck = Roka*
*Mercedes 1413-1414 truck = Bargazal*
*Mercedes 1312 (and similar sizes) truck = ‘Yar Fakas*
*Max Diesel = ‘Yar Rasha* (Kirar Kurma)
*Man Diesel (12-Wheeler) = Kwamanda*
*Truck with wooden body = Shorido*
*Hearse = Motar gawa*
*Towing van = Janwe*
*Tractor = Tantan/tarakta*
*Trailer = Titiri/tirela*
*pick-up van = A kori kura*
*Bulldozer = Katafila/buldoza*

See also  YA GANAWA KARENSA AZABA DON YA KOYA MAI DARASI

*SUNAYEN WASU YANKUNA DA HAUSA*

*Ibadan = Badun*
*South West Nigeria = Kurmi*
*Port Harcourt = Fatakwal*
*Onitsha = Anacha*
*Africa = Afirka*
America = Amurka
*Turkey = Turkiyya*
*Istanbul = Santabul*
*Parsia = Fasha*
*Russia = Rasha*
*Germany = Jamus*
*Britain = Birtaniya*
*Sierra Leone = Salo*
*Chad = Chadi*
*Cotonou = Kwatano*
*Port Lame = Fallomi*
*Yemen = Yamal*
*Israel = Isira’ila*
*China = Sin*
*Niamey = Yamai*

*SUNAYEN WASU ABUBUWA NA TURANCI DA AKA HAUSANTAR DA SU*

*Conductor* = Kwandasta
*Scrutiniser = Sakwaneza*
*Brake = Birki*
*Gear Box = Giyabos*
*Bumper = Bamba*
*Radiator = Lagireto*
*Carburator = Kafireto*
*Distributor = Disfuto*
*Coil = Kwayil*
*Valve = Bawul*
*Bearings = Boris*
*Rings = Ringi*
*Plug = Fulogi*
*Crank Shaft = Karanshaf*
*Grand Overhaul =Garanbawul*

*Sunayen Igbo da Yarabawa da Turawa da sauran kabilu wandanda Hausawa Suka Hausantar da SU*

*1) Tope = Takwai*
*2) Kingsley = Kirsili*
*3) Gbenga = Biyanga*
*4) Ifreke = Cikurege*
*5) Ngozi = Ingozi*
*6) Nwankwo = Nawanko*
*7) Gbagyi = Gwari*
*8) Luggard = Lugga*
*9) Bordeaux = Bod’o*
*10) Awolowo = Awwalaho/Auwalawo*
*11) Nnamdi = Namandi*
*12) Balat Hughes = Balatus*
*13) Taylor Woodrow = Tal’udu.*

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here