Majalisar Dokokin Kano ta bukaci a daina Rijistar sabbin Babura adai-daita

0

Majalisar Dokokin Kano ta bukaci a daina Rijistar sabbin Babura adai-daita

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin Kano ta haramtawa hukumar Karota yi wa sabbin baburan Adaidaita sahu rijista,

majalisar ta ce wannan wani mataki ne na shawo kan matsalar da ta kunno kai tsakanin masu sanaar baburan adaidaita sahu da hukumar lura da zirga-zirgar ababan hawa wato KAROTA, bayan da masu wannan sana’a suka shiga yajin aiki,

Hakan ya biyo bayan kudirin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kunci da Tsanyawa Garba Ya’u Gwarmai ya gabatar inda yace yin hakan zai taimaka wajen kawo karshen matsalolin da masu baburan a adaitata sahun ke haifarwa ta fuskar tukin ganganci ga gudun wuce saa da sauran laifuka da tuni ake kuka da su.

See also  An kama Manyan Dilolin Kwaya 100 A Jihar A Katsina

Ya’u Gwarmai ya kara da cewa ” kowa yana ganin irin yadda ‘yan adaidaita Sahu ake Kuka da su wajen kwace wayoyi ga rashin daa gashi za su cutar da kai amma idan kai masu magana za su ci mutuncinka komin darajarka su gaya maka magana”

A ranar litinin da Talata data gabata ne dai masu Baburan adaidaita sahu suka yi yajin aiki wanda ya haddasa mawuyacin hali ga jamaar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here