MAI MARTABA SARKIN DAURA YA CIKA SHEKARA 14 A KAN MULKI

0

MAI MARTABA SARKIN DAURA YA CIKA SHEKARA 14 A KAN MULKI
(1/3/2007-1/3/2021).

A jiya ranar Litinin 1 ga watan Maris 2021 Sarkin Daura Alh. (Dr) Umar Farouq Umar CON, ya cika shekara goma sha hudu (14) a kan karagar mulkin Masarautar Daura.

An gabatar da karatun Alqur’ani mai girma, tare da addu’o’i na musamman domin nuna godiya ga Allah.

Sarki ya gabatar da bayani gamsasshe da nuna farin cikinsa da Allah ya ba shi daukaka, girma da ikon sarautar Daura tsawon wannan lokaci, tare da samun nasarori masu yawa.

Sannan daga bisani Hakimai irin su Galadiman Daura, Sarkin Sudan, Ciroman Daura, Sarkin gabas, Fagaci, Shamaki Sarkin Dogarai, Sheikh Imam Malan Nazir Kofar Baru, Sheikh Imam Malan Hassan Yusuf da kin Limamai, sun gabatar da bayanai daban-daban da bayyana kyawawan dabi’u na Sarkin Daura irin su yawan kyauta, kyautatawa talakawa, son cigaban masarautar Daura, rashin girman kai, daukar shawara, son hadin kan al’ummarsa, son cigaban addinin Musulunci, tare da hade kan kawunan Darikun aaddini, adalci, gaskiya da amana. Sannan dukkaninsu sun yi fatan alkhairi da addu’ar Allah kara masa tsawon rayuwa mai albarka idan cikawarsa ta zo, Allah ya sa ya cika da imani, kuma Allah albarkaci zuri’arsa.

A cikin takardar da Sarkin Labarai, ya rubuta ya bayyana takaitaccen tarihin Sarkin da kuma wasu nasarori da ya samu a cikin mulkinsa kamar haka:

An haifi Alh. Dr. Umar Farouk Umar CON, Sarkin Daura na 60 a garin Daura ranar 5 ga watan Mayu 1933, kuma shi Da ne ga Marigayi Magajin Garin Daura, Umaru Dan Sarkin Daura, Abdurrahman Malam Musa. Sannan Mahaifiyarsa Hajiya Hindatu Muhammad ‘Yar Dansanwai Muhammad .
Mai Martaba Sarkin Daura, Alh. Umar Farouk Umar ya gaji Yayansa, Marigayi Sarkin Daura, Muhammad Bashar a ranar Alhamis 1 ga watan Maris 2007, a lokacin Marigayi Shugaban Kasa, Umaru Musa ‘Yar’adua yana Gwamnan Jihar Katsina.

An ba shi sandar girma mai daraja ta daya a ranar Asabar 22 Mayu, 2007.

Bayan ba shi sandar girma, Mai Martaba Sarkin ya shiga cikin tsare-tsare da gyare-gyaren gudanar da mulki gadan-gadan domin cigaban masarautarsa da kasa baki daya.

Cikin shekaru 14 da ya yi yana mulkin jama’a masarautar Daura ta sami gagarumin cigaba da ayyukan raya kasa kamar haka:

1~HADA KAWUNAN JININ SARAUTA DA DAURAWA A HARKAR MULKI: Ta hanyar janyo su da ba su sarautu domin ba da gudunmawa wajan cigaban masarautar, ta haka ya kara Hakiman Karaga, masu ba shi shawara, Hakimai masu Kasa daga 10-16, Magaddai/Dagatai daga 77-256 don kara kusanto da al’umma ga masu mulki.

2~SABON TSARIN SAUKAKAWA TALAKA: Ta hanyar fara kai koke ga Mai Unguwa zuwa Dagaci zuwa Hakimi, sannan a zo ga Majalisar Sarki da samar da sabbin ofisoshin Sakatare, Shugaban Ma’aikata, tarihi da yada labarai.

3~ILIMIN BOKO (ZAMANI): Mai Martaba ya dauki kwararru ‘yan Daura masu ba shi shawara a kan ilimin Firamare, Sakandire da manyan makarantu. Ya samar da cibiyar share fagen shiga Jami’a guda biyu (JAMB CENTRE) da aljihunsa. Ya tallafa wa dalibai sama da 1500 masu karamin karfi da kudin daukar jarrabawa na JAMB, NECO, NABTEB, DE.
Ya jajirce wajen tabbatuwar manyan makarantun gwamnatin Tarayyar na Daura Federal Polytechnic da Transport University.

4~ILIMIN ADDINI MUSULUNCI: Tun hawan sa karagar mulki ya dauki kudirin tabbatar da Shari’ar Musulunci, ya nada mashahuran Malaman kowace kungiyar addini wato Izala da Darika. Ya karfafa gina masallatan Juma’a a garuruwa da dama da ba da tallafin kudi da kayan aiki, a kowace Sallar Juma’a yana zagayawa masallatai don gaisawa da jama’a da sauraron matsalolin wuraran ibada.

Mai Martaba ya yi bakin kokari wajen hada kai da fahimtar juna tsakanin kungiyoyin addinai ciki da wajan kasar nan, kuma tsaye yake wajen fatattakar duk wata kungiya da take da’awah a kan abin da ya saba wa Al’qur’ani mai girma da Sunnar Ma’aiki (S.A.W).

5~LAFIYA: Mai Martaba Sarki ya kafa kwamitin sa ido a kan alluran rigakafi. Ya gudanar da ran gadi don fadakar da al’umma a kan cututtuka masu yaduwa kamar; HIV, EBOLA, CORONA VIRUS da sauran su. Ya jajirce wajen yaki da masu safara da ta’ammuli da miyagun kwayoyi.

6~SADA ZUMUNCI: Hakika Mai Martaba ya ba da mamaki wajen kokarin sada zumunci da Sarakunan Jamhuriyyar Nijar da Nijeriya a tsawon shekaru 14 masu albarka, akwai Sarakuna da dama wadanda Daura ba ta taba mu’amula da su ba, sai a lokacinsa.

7~TAIMAKON AL’UMMA: Wannan kuma wata baiwa ce daga Allah ya yi masa tun yana Yaro. Haka ya taso da son hidimtawa al’umma, wani lokacin sai ya ci bashi don ya ba da kyauta. Yana tallafawa masu karamin karfi da kudi, sutura da kayan abinci.

Mai Martaba Sarkin Daura saboda kwarewarsa Hikimarsa da jajircewa wajen hidimtawa talaka, an nada shi a matsayin mataimakin Amirul Hajj na kasa a 2007. Sai Amirul Hajj na Jihar Katsina a 2008, wanda ya sami yabo daga gwamnatin kasar Saudi Arabia da Nijeriya.

Masu hikimar magana suka ce; “Yabon gwani, ya zama dole”. Domin irin wannan kokari, hikima da kyakkyawar aniya, Mai Martaba Sarkin Daura ya sami lambobin yabo da dama daga kungiyoyi da gwamnatoci a ciki da wajen kasar nan.

Ya sami lambar karramawa daga gwamnatin Tarayya ta ba shi CON a 2008.

Allah ya ja zamanin Sarkin, ya kara masa basira da imani.

Usman Ibrahim Yaro
Sarkin Labaran Masarautar Daura

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here