MAHADI SHEHU YANA TSAKA MAI WUYA

0

MAHADI SHEHU YANA TSAKA MAI WUYA

… ‘Yan sanda na hanyar kawo shi Katsina
Zai fuskanci kotuna 3 a Katsina

Mu’azu Hassan
@ Jaridar Taskar Labarai

Alhaji Mahadi Shehu, dan kasuwa, mai kwarmato, dan Katsina mazaunin Kaduna da yake ta asakala da gwamnatin Katsina, yanzu haka yana cikin tsaka mai wuya.

A ranar 16/2/2021 bayan dawowarsa daga wata tafiya ya shiga jirgi a Kaduna zuwa Abuja, bisa kaddara ya shiga tare da wasu ‘yan kwarmato suka kira ‘yan sanda suka shaida masu.

Tafiyar daga Kaduna zuwa Abuja, duk wata ka’ida ta kama shi aka cika ta. Don haka yana isa Abuja aka yi caraf da shi.

Jaridar Taskar Labarai ta fara watsa labarin.

An tsare Mahadi Shehu a wani ofishin ‘yan sanda da ke Wuse Zone III. Aka soke belin da aka ba shi na kansa. Daga nan matsalar ta fara.

Mahadi Shehu ya shigar da kararrkin neman hakkinsa a kotu.

Kotu ta yi zama uku wanda Lauyoyin Mahadi kawai ke zuwa ban da na ‘yan sanda.

‘Yan sanda sun rubuto takarda a babbar kotun Katsina, wadda suka shigar da karar Mahadi Shehu suna neman a canza ranar da suka sanya na shari’ar daga 8/3/2021 zuwa 1/3/2021.

Mahadi Shehu ya sake shigar da wata takardar koke ga babban Jojin Kasa a kan kotu da kuma Alkaliyar da za ta yi masa shari’a.

A takardar, Mahadi Shehu ya bayyana cewa Alkaliyar na da alakar kut-da-kut da matar Sakataren Gwamnatin Katsina da kuma na Alhaji Dahiru Barau Mangal, takardar koken da har yanzu tana ofishin Babban Jojin.

Wata kotu ta yanke hukuncin a saki Mahadi kan beli, amma ‘yan sanda suka ce shari’ar da ta yanke hukuncin ba su halarta ba, kuma suna da wani umurnin kotun da ya wuce wanda ta ba da belinsa.

A yau Asabar 6/3/2021 ‘yan sanda sun baro Abuja da Mahadi Shehu zuwa Katsina, domin ci gaba da tsare shi har zuwa Litinin 8/3/2021 da za a gabatar da shi gaban kotu.

See also  NEDC to construct 500 housing units, schools for IDPs

A jawabansa da ya rika yi ana watsawa a yanar gizo, kuskure hudu Mahadi ya yi wanda daga lokacin suka dagula masa lamari.

Farko da ya sanyo Gwamnan Katsina a ciki balo-balo, kuma ya nuna sai ya ga bayansa.
Na biyu, sako Dahiru Mangal da ma fara nufarsa kai tsaye yana neman ya karya shi, inda babu gaba.

Na uku, sako Sarakunan Katsina da Daura.

Na hudu, yadda ya sanyo neman lalata shaksiyyar Dakta Mustapha Inuwa, abin da ya sanya Dakta Inuwa ya dau alkawarin shari’a ce za ta raba su, ko don ya gyara harkar siyasarsa.

Jaridar nan ta samu tabbacin a daidai lokacin da ya fara sabon fada da Dakta Mustafa Inuwa, wasu na kusa da shi sun samu ganawar sirri da Mahadi suka roki alfarma har ya amince ya tsagaita wuta a kansa.
har ma lokacin ya dan yi sanyi a kansa, ya karkata a kan wasu ciki har da wadanda ake ganin ba sa tare da Mustafa Inuwa din.

Duk mai bin jawaban Mahadi zai lura akwai lokacin da ya canza salo, ya kuma yi sauki a kansa.

Kamar yadda wata majiya ta tabbatar ma wannan jaridar kuma muka yi nazarin duk bidiyonsa.

A Katsina kotuna hudu ke jiransa, Babbar Kotun Tarayyar da wasu kotunan shari’a guda biyu, ko ya lamarinsa zai kasance? Lokaci ne zai tabbatar.

Mahadi Shehu hamshakin dan kasuwa ne, wanda dukiyarsa tana cikin biliyoyi ne, kamar yadda jaridar nan ta tabbatar.
________________________________________________
Taskar labarai na bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da jaridu biyu da suke tafiya tare katsina city news a www.thelinksnews.com da the links news www.katsinacitynews.com da duk sauran shafukan sada zumunta. Duk sako a aiko ga 07043777779 da kuma 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here