Mun kubutar da mutane 111 da dukiyar miliyan N180 a Kano

0

Mun kubutar da mutane 111 da dukiyar miliyan N180 a Kano– Hukumar Kashe gobara

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa ta yi nasarar kubutar da rayukan mutum 11, sai kuma dukiyoyin jama’a da suka kai Naira miliyan 180.2 a cikin ibtila’in gobara 95 da suka auku a jihar a watan Fabrairun da ya gabata,

Bayanin haka ya fito ne daga Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar, Sa’idu Muhammad a wata sanarwa da ya rabawa manema a yammacin Laraba,

Kakakin hukumar, ya kara da cewa an samu asarar rayuka takwas da asarar dukiya ta kimanin Naira miliyan 11.3 wacce goborar ta lankwame.

See also  500 persons benefit from FG’s electronic conditional cash grant in Anambra

Kazalika ya ce an kubutar da mutane 59 ta hanyar kiran wayar salula, sai kuma guda 13 da mazauna yankin suka gaza sanar da mu,” in ji shi.

Sa’idu Muhammad, ya bayyana cewa mafi yawan ibtila’in gobarar da suke aukuwa a Jihar na da alaka ne da sakaci kan kula da tukunyar girki ta gas da wadanda suka shafi na’urorin da ke amfani da wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here