WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE?

0

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE?
muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Gobe za a kai mahadi shehu Wanda yan sanda suka kawo daga Abuja domin fuskantar tuhumar da suka shigar a kansa kwanakin baya.
An kawo mahadi shehu a jiya asabar 6/4/2021 yan uwansa na jini sun fada ma jaridun taskar labarai cewa tunda aka kawo shi yan sanda sun hana a ganshi.yayi ikirarin an hana lauyoyin sa ganawa dashi.
Daya daga cikin su mai suna Ahmad Abubakar yazo har ofishin taskar labarai da yammacin nan na lahadi 7/3/2021 yace a jiya su je ofishin yan sanda domin kai masa abinci amma anki amincewa su ganshi balle su bashi abincin.yace yau ma sun kai masa anki amincewa su bashi
Yace sun kai masa katifa domin mahadi na fama na ciwon lakkar gadon baya yan sanda sunki yarda a bashi katifar
Ya kara da cewa mahadi na fama da wasu cututtuka ciki har da hawan jini Wanda duk inda zashi da magungunan sa.sunyi zargin har yanzu ba a bashi magungunan sa ya sha ba.
Yan uwansa sunyi Kira ga jami an tsaro su tabbatar an baiwa mahadi kariya sosai don kar wani abu ya same shi.
Sunyi zargin cewa ana tsare da mahadi a yanayi mafi kunci da ya taba gani a rayuwarsa.kuma dan Adam zai ba iya rayuwa a ciki ba.suka yi zargin Daki ne mai dattin gaske nan yake kashi da fitsari.ga kyankyasai na yawo
Yan uwan sunyi Kira da a kula da lafiyarsa kuma a bashi kariya gobe domin akwai yiyuwar wasu mafusata na iya yunkurin taba lafiyar sa.in ba a dau mataki ba.
WACE KOTU ZA A KAISHI?
Mahdi na fuskantar shara a uku daya a babbar kotun tarayya dake nan katsina wadda mahadi ya rubuta takardar koke aka mai shara ar yayi zargin ba zatayi masa adalci ba. kuma zata yi zamanta gobe.8/3/2021.
Akwai kuma shara ar dake gaban kotun daukaka kara ta jaha wadda mahadi ya shigar ita kuma zatayi zamanta a gobe a garin Dutsinma.
Sai kuma daya a wata kotun shara ar musulunci. Cikin ukun na kowacce za a kai mahadi shehu a gobe?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here