AN SALLAMI SHUGABAN NIMET DAGA AIKI.

0

AN SALLAMI SHUGABAN NIMET DAGA AIKI.
………..Bullar wasu bidiyo guda biyu ne sanadi?
Muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Ministan sufuri da harkar jiragen sama Alhaji Hadi sirika bisa amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami shugaban hukumar kula da yanayin sama ta kasa( NIMET) farfesa sani mashi daga aiki.
Majiyarmu ta tabbatar mana cewa Ministan ya shaida ma farfesa sani mashi ya mika ragamar shugabancin hukumar ga mafi girman mukami a a ma aikatar .
Majiyarmu tace shugaban kasa ya umurci ministan na harkar jiragen sama ya duba Wanda ya dace a bi duk kaidojin da suka dace a nada shi.
Majiyarmu tace wasu bidiyo guda biyu suka fara haifarwa da shugaban hukumar matsala.bidiyon farko na inda aka nuno wata da ake zargin diyarshi ce tana lika kudin dala a wani buki na ya yan farfesan. Bidiyon da jaridar katsina city news suka samu kuma suka Dora shi a bisa shafinsu.
Bidiyo na biyu inda aka ruwaito shi aka kuma nuna shi a wani taro a garin mashi yana jinjina da yabo akan shugaban jam iyyar PDP ta katsina Alhaji salisu yusufu majigiri. taro da ake zargin yan jam iyyar PDP suka shirya shi .farfesan ya halarta kuma yayi magana kamar Dan pdp Bidiyon Wanda jaridar taskar labarai ta yada shi .
Majiyarmu tace an fara binciken farfesa sani mashi akan alakar da ake zargi yana da ita da PDP a boye da kuma baiwa wasu jiga jigan yan PDP kwangila domin Raba kafa a tafiyar 2023.
Wata majiya maras tabbas tace ya na fara shirin takarar sanata a yankin daura a 2023..
Majiyarmu tace an kuma binciki wasu zarge zarge akanshi wasu ma suna a hukumar EFCC da ICPC, wannan ya Sanya ministan ya rubuta takardar neman amincewar cire shi ga shugaban kasa kuma aka amince masa.
Daga zargin da ake masa baya taimakon yan jam iyyar APC da sukayi wahala. Ya dauko wani jigo a jam iyyar PDP mai suna Ali Haro jani shine mai bashi shawara. Kamar yadda majiyarmu ta shaida mana
Gobe litinin 15/3/2021 ake Sanya ran zai bar kujerar tasa a hukumance .zai Mika shugabancin wajen ga mafi girman mukami a hukumar.
Ko bincike akansa zai ci gaba in ya bar ofis ? Lokaci ne zai nuna
________________________________________________
Jaridar taskar labarai na bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da yan uwanta katsina city news dake www.katsinacitynews.com da the links news dake www.thelinksnews.com duk sako a aiko ga 07043777779.ko 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here