Yadda Farfesa Abdallah Uba Adamu ya samu sarautun Gargajiya a kudancin Kasar nan

0

Yadda Farfesa Abdallah Uba Adamu ya samu sarautun Gargajiya a kudancin Kasar nan

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

A shekarun da ya shafe yana jan ragamar Jami’ar Karatu daga gida ta NOUN Farfesa Abdallah Uba Adamu ya samu karramawa daga sarautun gargajiya a masarautun gargajiya na kudancin kasar nan, wadanda suka hada da:

Sarautar farko da aka bashi i ta ce: (Nze Okaa Omee) mai maanar ‘Mai tsayayyar magana’ an bashi ne a ranar 27 ga watan Satumba 2016 a taron Offalla da ya gudana a jihar Inugu.

Karramawa ta biyu ita ce (Oruakpar Emevor) da ya ke nufin ‘Mai bunkasa cigaban al’umma’ wanda alummar Emevor suka ba shi, a ranar 8 ga watan July 2017 a jihar Delta.

Ta uku a cikin sarautar shi ne (Ezi Ekwareazu) da take nufin ‘Abokin mutanen Ekwareazu’ da aka bashi a wajen taron yiwa kasa hidima, a ranar 8 ga watan oktobar 2019 a jihar Imo.

Sarauta ta hudu ita ce (Abba ji Nmusa) maanar ta shi ne ‘mai ‘kimanta darajar Ilimi’ wanda basarake Asaga Ohapia ya bashi a jihar Abia a ranar 5 ga ga watan Fabrairu 2021.

Wadannan sarautu duka Farfesa ya samesu ne a cikin shekara shida da yayi a wannan Jam’ia ta NOUN wanda ya kafa babban tarihi a kasa, Babban burin farfesa shi ne samar da ingantaccen Ilimi a kasa baki daya ba tare da bambancin kabila ko addini ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here