KATSINA: TATTALIN ARZIKI DA MAKOMAR TA

0

KATSINA: TATTALIN ARZIKI DA MAKOMAR TA. {1}

_Sharhin; Katsina City News_

Jaridun *Katsina City News* sun zauna sun yi nazarin jawo hankalin al’ummar Jihar Katsina lokaci ya yi da za su zauna su yi nazari, tsari da aiki tukuru na makomar Jihar nan a gaba, cigabanta da al’ummarta da kuma ‘yan baya masu zuwa.

Jihar yanzu tana da sama da mutane miliyan tara, ita ce ta hudu a yawan al’umma kasar nan. Tana da ma’aikata na Jiha da Kananan Hukumomi kasa da dubu 100.

Kason da take samu daga gwamnatin Tarayya kashi 55% zuwa 60%, yana tafiya ga albashi ne. Kashi 20 yana tafiya ga gudanarwar tafiyar da gwamnati ne.

Kudin da ya rage wa Jihar in an yi wancan cire-cire ba ya wuce kashi 20% da ‘yan kai.

Cikin su ake sace wasu, wasu kuma a ce za a yi aikin raya kasa da su.

Ayyukan sun hada da gina hanyoyi, ba da magani, gina asibitoci, makarantu da sauransu. Su ma a sace wasu, a yi aiki da ‘yan kadan.

Katsina ce mafi koma baya ga tsarin samun kudin shiga a kasa nan a cikin jihohi masu yawa.

Ga misali, Jihar Legas mai yawan mutane miliyan 14 da doriya, sun tsara cewa daga nan zuwa 2025 ba su bukatar kason kasa kafin su rayu. Kaduna, Kano, Fatakwal duk sun yi wa kansu tsari na rayuwa ba tare da kudin man fetur ba. Me Jihar Katsina ke ciki?

Yawan jama’a albarka ne, in aka yi amfani da su daidai wadaida.

A Legas mafi yawan kudin da suke tarawa na gudanarwa suna samunsu ne daga yawan jama’a da suke shigo. Kudin raya kasa kuma daga kamfanoni ne. Me muke ciki a Jiharmu?

See also  An Cire Najeriya Daga Cikin Kasashen Da Zasu Amfana Daga Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro Na Afirka

Ana fitar da haraji daga ma’aikatan gwamnati, wanda kai tsaye ake cire masu kafin a biya albashin ma’aikatan nan da ake ma wannan cirewa ba su kai yawan dubu 100 a duk Jihar da Kananan Hukumomi ba, kuma kudin suna da tsarin yadda ake raba su tsakanin gwamnatin Jiha da Tarayya.

Sauran haraji na ‘yan kasuwa da kamfanoni da ababen hawa, babu wani tsari mai inganci da diddigi da tantancewa na amsar su har su shiga cikin aljihun gwamnatin Jiha da kuma amfani da su kamar yadda ya dace. Mafi yawa yana biyan bukatar wasu masu kula da hukumomin karbar harajin ne.

MEYE MAFITA?

Duk duniya kowace kasa, Saudi Arabiya, Iran, Senegal, Iraqi da Pakistan, ko kasashen Turai da Amurka da Asiya, suna da tsarin kudin shiga, kuma wanann kan ba ‘yan kasa damar su kalubalanci gwamnatocinsu, domin kuma da dukiyar albarkar kasa da kuma tasu ake gina kasar.

A shekarar 2017 mun gani da jin yadda a kasar Saudiyya aka kama wasu manyan Attajirai bisa zargin kamfanoninsu ba su biyan harajin da ya dace.

*MEYE MAFITA A JAHARMU TA KATSINA?*

Kudin man fetur da ake takama da shi, kullum rage daraja yake, kuma rashin zaman lafiya da kokarin canza fasalin kasa da ake neman yi ya sanya babu tabbacin nan gaba za a ci gaba da samun wannan kason kudin man fetur da ake bukata.

Ga sojan sa kai na yanki-yanki da ke ta bijirowa suna zama barazana ga Tarayyar Najeriya. Jihar Katsina ina mafita a tattalin arziki da cigaba?

Ku biyo mu a rubutu na gaba don cigaban nazarin mu, amma kafin nan a tattauna wannan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here