An fara Gasar Karatun Alkur’ani ta Kasa a Kano

0

An fara Gasar Karatun Alkur’ani ta Kasa a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

A yau juma’a 18 ga watan aka kaddamar da gasar Karatun Alkur’ani ta kasa a Convacational Arena da ke jamiar Bayero ta Kano,

Musabakar wacce ita ce karo na 35, ana gabatar da ita ne duk shekara da Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ke shirywa.

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne suka zama manyan baki na musamman, yayin da yan takara da manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan suka halatta,

An dai fara karfe hudu na yammacin yau da aka fara daga ‘yan takara izifi 10. sannan zaa yi bikin rufe gasar a ranar Asabar ta sama wanda ya yi daidai da 27 ga watan da muke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here