Gwamnonin Arewa ya kamata Ɗauki Matakin Bai Ɗaya Akan Matsalolin Tsaro a Arewa..

0

Gwamnonin Arewa ya kamata Ɗauki Matakin Bai Ɗaya Akan Matsalolin Tsaro a Arewa… ACSC

Majalisar Tuntuɓa Da Haɗaka Ta Arewa (ACSC) ta nuna alhinin rashin jindaɗin ta bisa ƙaruwar ayyukan ta’addanci a Lardin Arewa musammam a fannin ilimi.

A hakikanin gaskiya, ba ƙasar da, ko Al’umma da zasu sami duk wata Ci gaban Siyasa, Tattalin arziki da samun Ƴancin gudanar da harkokin addini a cikin irin wannan yanayi na tashin hankali, don haka bamajin daɗin abinda ke faruwa a Arewa. Bama iya barci saboda baƙin cikin halin da Ilimi da Tattalin arziki suka shiga yayin da ta ko’ina ake kaiwa makarantu hari domin wannan babban abin damuwa ne.

Don haka, mu a ACSC Muna kira Gwamnonin Arewa da su kawar da banbancin dake tsakanin su domin su haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen kawo ƙarshen ayyukan Ƴan Ta’adda a Arewa.

Hakazalika, ya zama wajibi ne a Samar da hukumci mai tsauri a kan masu aikata ta’addanci, kana muna yabawa da ƙoƙarin da hukomin tsaro suke yi don ganin an kawo ƙarshen ayyukan Ta’addanci a Arewa.

See also  5 NEW MEGA POWER STATIONS IN ABUJA TO BE COMMISSIONED IN DECEMBER 2022!

Bugu da kari, muna kira a garesu da su dage, su mayar da hankali kan ayyukan su, kuma su girmama dokokin ƙasa, su saka kishin ƙasa a lokacin aiki, kana su kiyaye dokokin kare haƙƙin Ɗan Adam a kan mutanen da babu ruwan su akan abinda ke faruwa na ta’addanci a yankunan su.

A Ƙarshe, ACSC muna yajajantawa Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari da Gwamnan Jihar Benue Mista Samuel Otom bisa iftilain daya faru, Muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya kare su, ya kare mana Al’ummar mu, Ya Allah ya kare Mairtaba da duk wanni mummunan nufi, bayan haka muna Jajantawa ga Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar lll da Gwamnatin Tarayya, bisa rasa rayuka da dukiyoyi da aka yi a Arewa, kuma da yin addu’ar fatan Allah ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya”.

Injiniya Dakta Haris Jibril
Shugaban ACSC ta ƙasa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here