Duk wani gini da aka yi a filayen da ba su dace ba a Kano za mu rushe shi cikin kwana 100—Sabature
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Kakakin dan takarar Gwamnan Kano a zaben 2019 da ya gabata, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar, idan Allah ya basu nasara a zaben Gwamnan Kano a shekarar 2023, a cikin kwana darin farko zasu rushe duk wani gini da aka yi a filayen da basu kamata ba.
Sakon da ya wallafa da turanci, Bature ya kara da cewa, za su cire dukkan sabbin Sarakunan da aka kirkiro a Kano, tare da dawo da Khalifa Muhammadu Sunusi II kan karagarsa a matsayin Sarkin Kano guda daya tilo.
Kazalika ya ce “Ina tabbatar maku da cewa kwana darin farko zai kasance kwanakin Rusau ne a jihar Kano, inda za mu bi duk wani fili ko gini da aka yi ba bisa kaida ba za mu rushe shi” a cewarsa.