BA A SULHU A CIKIN SAUKI

0

BA A SULHU A CIKIN SAUKI
…..darasi daga shekau boko haram
@ jaridar taskar labarai.
Wani littafi da wasu turawa yan jarida suka rubuta, mai suna brings back our girls, the untold story of global search for Nigeria missing girls by Joe Parkinson and drew henshaw.
Wanda yanzu ake sayar dashi a yanar gizo ta kamfanin Amazon.littafin ya bayyana abun da ba a fada ba a kokarin kwato daliban makarantar Chibok daga hannun yan boko haram.
Wani darasi abin dauka a halin da ake ciki na barayin daji masu dauke da makamai shine.
Shekau shugaban boko haram ya kafe ba zai bayar da yan matan ba.
Amma a 2016 lokacin da gwamnatin Buhari ta sanyo shi gaba ta sama da kasa da ruwa, kudi da abinci sukayi ma sansanonin shi wahala.
Shekau da rundunar sa suka zama Rana zafi Inuwa kuna yaga baya da wata mafita da kanshi ya nemi a tattauna akan sakin yan matan Chibok. Bisa sharuddan da zai samu saukin halin da yake a ciki.
Tattaunawar da ta kai aka saki wasu daga cikin su a zango biyu.
Shekau ya fahimta cewa sararawar shi ya samu sauki a lokacin shine ya bude kofar tattaunawa kuma makaminshi sune yan matan Chibok. Dasu yayi amfani.
Marubutan suka ce da a lokacin shekau na kan samun nasara. Babu yadda zai amince da wata tattaunawa.

Hotunan yan matan lokacin da yan boko haram zasu mika su

Hoton ganawar ido da ido da Jami an sulhu Dana boko haram

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here