YAN BINDIGA SUNKAI HARI TAKUM-MOSA TA JIHAR OSUN.

0

‘YAN BINDIGA SUNKAI HARI TAKUM-MOSA TA JIHAR OSUN.

…mutane da yawa sun rasa rayukan su.

Da misalin karfe 8:00pm na daren ranar alhamis 25-03-2021 wasu mahara dauke da miyagun bindigu suka kai hari Iyere (Store) dake cikin yankin karamar hukumar Atakum-mosa ta jihar Osun. Maharan sukai farmakin ne a store mazaunar ‘yan arewa masu hakar zinari. Ganau ya tabbatar mana da cewa suna zaune cikin wani shago na Malam Sadiku wanda haifaffen Daura ne ta jihar Katsina Kuma dila ne na zinari, sai suka ga wani mutum ya fado masu dauke da sanda da adda suka ce masa lafiya zaka shigo mana da makami bayan kasan ansaya dokar hana yawo da adda ko sanda, daga nan Kuma sai sukaji karar bindigu na tashi, wanda nan take suka fasa wata hanya suka gudu duk da cewa sunbi su da harbi amma dai Allah ya tseratar da su. Sai dai sun kwashe miliyoyin kudi da zinare da wayoyin hannu na mai shagon watau Malam Sadiku Daura. Amma sunyi garkuwa da Usman Damari wanda shima dilan zinari ne da wasu mutane masu yawa, ya zuwa hada rahoton nan mun samu labarin cewa sun nemi basu kudin fansa naira miliyan hamsim N50,000,000 sannan su sako su.
Bayan sun gama da store sai suka tarbe babbar hanyar da ta taso daga Akure zuwa Lagos wanda baidi nisan 2km daga barikin sojoji, inda canma suka yi ta harbin motoci amma dai bamu samu labarin asarar rayuka ba. Duk dai a ranar ta alhamis ansamu asarar rayukan mutane tara a Kauyen Aruwan, sanadiyyar fashewar silindar gas ta walda inda gobara ta tashi nan take har lamarin ya kazamce haka
A wani labarin kuma mutane bakwai sun rasa rayukan su sanadiyyar zabtarewar kasa da ta rutsa dasu a cikin ramin hakar zinari a Ijana, dama sati biyu da suka wuce irin wannan zabtarewar tasa mutum talatin da biyar sun rasa rayukan su. Irin wannan lamari ya dade yana faruwa a yankin duk da taka tsan-tsan da masu hakar zinare ke cewa suna yi domin kauce ma faruwar irin haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here