SAKE NADIN DIKKO RADDA DG SMEDAN
….Anyi taron addu a da farin ciki
@ katsina city news
Wasu kungiyoyi Goma karkashin Gidauniyar gwagware Foundation. Sun gudanar da taron addu a da nuna farin ciki da sake nada Alhaji dikko Radda gwagwaren Katsina shugaban hukumar smedan
Taron an gudanar dashi a farfajiyar karamar hukumar charanchi a ranar asabar 3/4/2021 da misalin karfe takwas na safe zuwa sha biyu da rabi na Rana.
An fara taron da budewa da du a i, sai saukar karatun alkur ani mai tsarki.sai addu o i na musamman da akayi.
Sannan akayi wani Dan takaitaccen barkwanci Wanda babu kida ko waka a cikin shi.
Daga nan sai aka gabatar da jawabai, Wanda manyan baki suka gabatar.
Daga cikin wadanda suka gabatar akwai kwamishinan ilmi na jahar katsina faresa Badamasi lawal charanci inda a jawaban sa yayi addu a da fatan Allah ya ba dikko Radda gwamnan katsina.
Shi kuma Alhaji Ibrahim ma ajin gwagware Foundation ya kawo yadda shugabancin dikko Radda a hukumar smedan ta kawo alheri a kasar nan baki daya da yadda hukumar ta kawo dauki ga tattalin arzikin al umma a kasa baki daya.
Alhaji Ibrahim yayi godiya ga shugaban kasa da tabbatar masa cewa gwagwaren katsina ba zai bashi kunya ba.
Shi kuma shugaban Gidauniyar gwagware Alhaji kabir amoga.ya bayyana irin ayyukan Alheri wadanda Gidauniyar ta gwagware ke aiwatarwa.kuma ya jaddada cewa aikin Alheri likkafa Zata kara gaba.
Malamai kuma sun gabatar da nasihohi na jin tsoron Allah da tara gaskiya ga sabon Wanda aka sake nadawa Alhaji dikko radda
Alhaji Dikko Radda shine a tarihin hukumar smedan zai rike mukamin har karo na biyu.
Manyan mutane a ciki da wajen charanci suka halarci taron.![]()
![]()