TAKARDAR NADIN KOGUNA HARAMTACCIYA CE.

0

TAKARDAR NADIN KOGUNA HARAMTACCIYA CE.
Suleiman Umar
@ katsina city news
Wata takarda da masarautar katsina ta fitar a yau litinin 5/4/2021 ta bada sanarwar sarautar koguna, takardar haramtacciya ce bisa dokar aikin gwamnati.
Takardar da ta sanar da ba Alhaji kabir Garba kijibta sarautar kogunan katsina tsohon koguna ya rasu a ranar 1/4/ 20201 akayi Jana izarsa ranar 2/4/2021
Takardar bada sabon koguna an fitar da ita da Sanya mata hannu a ranar litinin 5/4/2021 wadda take ranar Hutu ce, kuma a bisa doka duk wani aikin Ofis a ranar haramtacce ne.kuma duk takardar da aka fitar haramtacciya ce
Jaridun mu sun tuntubi wasu tsaffin ma aikatan gwamnati da kuma lauyoyi masana Shari a , sun tabbatar ma da jaridun mu cewa.idan ba a chanza ranar ba, zuwa wata Rana ta aiki to duk abin da za ayi da ya danganci wannan nadin haramtacce ne.
Wani lauya yace abin da masarautar katsina ya kamata tayi ta chanza takardar da kuma ranar zuwa ranar aiki.amma ranar 5/4/2021 ranar Hutu ce a dokar kasa.ga duk wani ma aikacin gwamnati da aikin gwamnati.
@ katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
Duk sako ga 07043777779
081377777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here