???????? ??????? 450: ?????????, ??? ????? ?? ???? ??? ???!
Daga Suleiman bala idris
Wannan labarin da zaku karanta ya faru da gaske, ba tatsuniya ko ƙage ba ne.
Ni ne mutum na farko da ya fara shiga tsakanin Zainab Ibrahim da ‘yan jarida (bayan ta fara shiga rigingimu). Zainab Ibrahim wacce ta shahara da suna Ummi Zee Zee, da kanta ta buƙaci hakan daga gareni, duk da kuwa a lokacin bai fi shekara biyu da na shiga harkar Jarida ba.
Wani abu ne ya faru a watan Janairun shekarar 2009 lokacin ina Editan Mujallar MATASA (wata Mujalla da ta yi tashe lokacin mulkin Marigayi ‘Yar’adua) wacce kamfanin Katsina Media Links mallakin Mallam Danjuma Katsina ke wallafawa.
Mun buga wani labari a shafin ????????? ??? ???????, mai taken: ??????? ?????-????? ?? ??????: ??????? ???? ??????? ??? ?????.
Ni na rubuta labarin bayan dogon nazari kan yadda harkar shan miyagun ƙwayoyi ta raunata rayuwar mawaƙi Lil Wayne, kuma a wancan lokacin shi ne abin koyi ga matasa.
A kan wannan labarin ne Ummi ta kira ni, tana nuna rashin jin daɗi, a cewarta wai mun zagi mawaƙi mai tasiri a duniya. Ni ban ma santa ba, saboda ban san kowa a harkar fim ba. Ta gama faɗin ra’ayinta sannan ta kashe waya. Kafin ta fara magana ta gabatar min da kanta da sunan Zainab Ibrahim (ba ta ce Ummi Zee Zee ba).
Bayan kaman kwana biyu, sai aka sake kirana da wannan lambar ta Glo, ban yi ‘saving’ layin ba, amma ina gani na iya tuna an kirani da lambar. Tana magana cikin isa da izza ta ce, Zainab ce. Na ce, Allah sarki! Nan ne ta fahimci ban ma yi ‘saving’ lambar ba. Ta cika da mamaki, ta ce, ‘ka yi laifi biyu. Na farko kun zagi Lil Wayne, na biyu ka ƙi saving lamba ta.’ Sai muka yi dariya.
Lokacin da za ta kashe waya, bayan mun gama magana, sai take ce min ai ‘yan jarida na da ƙarfin ikon gyara abu ko ɓata shi. Za ta so idan ta dawo Nijeriya mu tattauna. Lokacin tana Ƙasar Misra ta je hutawa. Ni a lokacin ba ta ita ma nake ba, saboda kaina ya ɗau zafi, muna kici-kicin tsara Mujallarmu ta watan Fabrairun 2009.
Bayan watanni kaman uku sannan na gane ashe Ummi Zee Zee ce Zainab Ibrahim ɗin da ke kira. A ranar da wani ke faɗa min cewa ita ce, a rannan ta sake kirana a waya. A ranar muka fara haɗuwa. Ta gabatar min da wasu ƙorafe-ƙorafe kan abubuwan da ake wallafawa a kanta. Ta nuna min wasu gidajenta a garin da muka haɗu (ba Kano ba).
A lokacin da gaske akwai ‘yan kuɗaɗe hannun Ummi, sai dai ba zan iya cewa sun kai nawa ba. A lokacin tana hawa motoci guda shida da ”customized number’ mai ɗauke lambobi Zee Zee 1, 2, 3, 4,5, 6. Da su take yawo a Kano, Kaduna da Abuja.
Mu’amalata da Ummi kawai harkar jarida ne. Duk da a lokacin ba ni da wata cikakkiyar gogewa a harkar Jarida, amma na yi ƙoƙari wurin ba ta shawarwarin da nake ganin ba kawai a harkar Mu’amala da ‘yan jarida ba, zai taimaka mata wurin mu’amala da mutane da sauƙake rigimar da take faɗa wa.
Lokacin da tsohon saurayinta ‘Ɗan Chana’ ya sakota gaba, ni ke bada shawarar me za a yi, me kuma za a rubuta. A lokacin tana tsananin bani tausayi ne, saboda irin tarin rigingimun da ke kanta. Har ta kai wasu cikin ‘yan uwanta sun sanni.
Ta sake fuskantar sabon babin rigima ne bayan da ta koma Fatakwal (Porthacourt) da irin abubuwan da suka shiga tsakaninta da su Timaya, Jonah de Monarch da Weatherman. Da gaske ne Timaya ya amshi kuɗaɗe hannunta da sunan waƙa da soyayya.
Akwai wani abu da ya faru har ta kai na shiga tsakani. Jonah De Monarch wanda suka yi waƙar ‘Janglover’ tare ne ya so ya damfareta, ƙarshe dai ni aka nema na shiga tsakani, har sai da ta kai Jonah ya yi ta surfa min zagi. Ƙarshe na ce mishi, ni ba ɗan fim ba ne ko mawaƙi, ni ɗan Jarida ne.
Na kawo kaɗan cikin waɗannan misalin ne don na tabbatar da cewa da gaske ana iya damfarar Ummi, saboda tana da saurin yarda. Amma ko ni ban yarda cewa an damfareta Miliyan 450 ba.
Akwai wasu ‘yan jarida da ta amince musu ta ba su kuɗi (ta faɗa min nawa ta basu) amma suka wallafa wasu hotunanta marasa kyawun gani da Timaya da Jonah de Monarch.
Saboda gajiya da shiga rigima ne dole ƙarshe na daina shiga waɗannan rigingimun muka kuma daina magana da Ummi. Kuma ma dai, lokaci ya fara yi min ƙaranci; ga aiki, ga karatu duk a lokaci guda.
Kafin mu daina duk wata mu’amala da ta shafi harkar jarida da Ummi na ba ta wasu shawarwari kan yadda za ta kaucewa ci gaba da faɗa wa irin waɗannan rigingimun. Musamman ma lokacin da labarin ‘soyayya da IBB’ ta yi ta yawo.
Mutane da dama sun tambaye ni kan me ke faruwa har Ummi ke son kashe kanta. Na yi ƙoƙarin bada amsa da ‘ni ma ban sani ba, rabona da yin waya da Ummi tun 2012’. Don haka nema na yi ƙoƙarin nemanta don jin dalilin da ya sa take son kashe kanta, wannan kafin labarin damfara ta fito kenan.
Zai yiwu ba gaskiya bane an damfareta Naira Miliyan 450, amma a yanzu ita ‘patient’ ce ta ‘depression’. Mai jinya ce da take buƙatar taimakon duk wanda zai iya taimaka mata har ta dawo hayyacinta.
Kamar dai yadda ‘yan Nijeriya da yawa ke fama da jinyar damuwar da ba su iya sanar da kowa. Mutane sun faɗi ra’ayoyinsu; masu kyau da munana. Gabaɗaya mun manta cewa, idan ƙarya Ummi ta yi kan damfarar da ta yi iƙirari, kenan ana da cikakkiyar hujjar da ya kamata a taimaka mata ta ga likita ko ƙwararre kan harkar da ta shafi ƙwaƙwalwa.
‘Depression’ gaskiya ne, musamman ga mutumin da ya saba da kuɗi kuma ya zo bai da su. Allah Ya sa mu gama da duniya lafiya!
Sulaiman Bala Idris
07-04-2021