Matsalar Tsaro: Ƙarya MURIC Ta Faɗi Kan Majalisa Ta 8, Inji Dr. Saraki
Daga Muhammad Abubakar, Abuja
Tsohon Shugaban Majalisa ta Takwas a Majalisar Dattawan Nijeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya mayar da martani kan wani iƙirari da Shugaban Ƙungiyar MURIC, Farfesa Ishaƙ Akintola ya yi.
Tsohon Shugaban Majalisar ta Dattawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Dr. Saraki ya bayyana wannan sanarwar manema labarai da MURIC ɗin ta fitar a matsayin ‘farfaganda mai cike da yarfe da ƙarairayi. Saraki ya faɗi haka ne yau a Abuja a wata takardar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Oluwole Onemola, ɗaya cikin masu taimaka masa kan harkar yaɗa labarai.
Saraki ya ce, batun da Farfesa Ishaƙ Akintola ya fitar na cewa Majalisa ta Takwas ce ta daƙile yunƙurin Shugaba Buhari na son sayo makaman Dala Biliyan 1, ba komi ba ne face ƙoƙarin maye gurbin gaskiya da ƙarya. “Wannan zunzurutun ƙarya ne. Ba a taɓa yin wani lokaci da Majalisa ta takwas ta daƙile yunƙurin fitar da kuɗi don sayo makamai ba, mun dai dage akan cewa duk wani kuɗi da za a fitar dole ne a bi ƙa’idar da ta dace.”
Dr. Saraki ya jaddada cewa: “A ranar Laraba 25 ga watan Afrilun 2018, a matsayina na Shugaban Majalisar Dattawa na karanta wasiƙa a gaban Majalisa daga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wacce a cikinta ya nemi a sakar masa kuɗi cikin gaggawa wanda sun kai dala 496,374,470. An ce kuɗin za a biya su ne kai tsaye ga asusun gwamnatin Amurka.
“Sai dai kuma a kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda shi ne madogarar duk wani aiki da muke yi, a cikin wannan kundin an zayyana cewa duk wani abu da ya shafi irin wannan harkar yana ƙarƙashin kulawar majalisar ƙasa ne. Kuma babu inda aka ce shugaban ƙasa zai ba majalisa irin wannan umurnin. Wannan na nuni da cewa, tun farko Shugaban Ƙasa bai bi ƙa’idar da ta dace ba. Amma duk da haka Majalisa ta bayar da umurnin sakin kuɗin. Kuɗin da MURIC ke magana wato Dala biliyan 1, Majalisa ta takwas ta bada umurnin sakinsu.
“Haka nan kuma idan ana iya tunawa, Gwamnatin Amurka ta yanke hukuncin daina sayar da manyan makamai ga Nijeriya bisa zargin take haƙƙin ɗan Adam daga ɓangaren sojojin Nijeriya. Bisa wannan ne ma wakilan majalisar Amurk suka zo Nijeriya a ranar 28 ga watan Agusta inda suka zauna da wakilan Majalisar Nijeriya; a nan ne muka roƙe su da a janye wannan hukuncin kuma za mu yi bincike kan zargin tare da tabbatar da rashin afkuwar irin haka a gaba.
“Sai bayan wannan zaman da muka yi da wakilan Majalisar Amurka bisa jagorancin Sanata Chris Coons da Ambasada Symington sannan Amurka ta yarda ta janye dokar daina sayar da makamai ga Nijeriya. Kuma bayan zaman namu ne, Majalisar Amurka ta ba Shugaba Trump shawarar a sayarwa da Nijeriya jiragen yaƙi na TUCANO.” Inji shi.
Ya ƙara da cewa, ɗaya daga cikin ƙoƙarin Majalisa ta 8 ne ya sa a lokuta da dama suka gayyaci shugabannin ɓangarorin tsaro su bayyana gaban Majalisa don a tattauna irin gudummawar da suke buƙata a fagen daga. “Misali a ranar 3 ga watan Fabrairun 2016 shugabancin majalisa ta takwas ya zauna da shugabannin ɓangarorin tsaro. Haka ma a ranar 8 da 12 ga watan Fabrairu Majalisa ta 8 ta shirya wani taro na musamman kan tsaro wanda cikin mahalarta taron akwai Mai ba shugaban Kasa Shawara kan harkar tsaro, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da sauran shugabannin ɓangarorin tsaro.
Daga ƙarshe dai tsohon Shugaban Majalisar ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da zantukan MURIC, domin cike suke da son rai, yarfe, da ajandar ɓata suna.