MARIGAYI MAHMUD TUKUR DA SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI
…Dalilin Rabuwarsu
Danjuma Katsina
@ jaridar Taskar Labarai
A shekarar 1983 Janar Muhammadu Buhari ya zama Shugaban Kasa ta hanyar juyin mulkin soja, Mahmud Tukur na cikin Ministocin gwamnatin masu karfi da tasiri. An kifar da gwamnatin Buhari a watan Agusta 1985, Mahmud Tukur na cikin wadanda ba su yanke dangantaka da Buhari ba. Shi ne ma ya rika shiga tsakanin Buhari da al’umma lokacin yana tsare a gidan Yari.
Lokacin rasuwar Mahaifiyar Muhammadu Buhari, lokacin shi yana tsare, da Mahmud Tukur aka yi komai, tun daga jana’iza har zuwa zaman gaisuwa.
Bayan an sako Muhammadu Buhari daga tsarewa, sai suka rabu da matarsa, Mahmud Tukur ne ya samar masa mata kyakkyawa Bafullanata daga Jihar Adamawa. Yarinya kuma ’yar’uwarsa.
A zaman da ya yi na shugabancin Hukumar PTF, Mahmud Tukur na gefensa, wasu ma sun ce yana cikin kusoshin fulogan da suka kawo nasara a aikin Hukumar PTF.
Yana Hukumar ne ya rubuta wani littafi, wanda har Majalisar Dinkin Duniya an kai kwafinsa.
Littafin ya fassaara da sharhi ne a kan wata wasika da Sayyadina Ali (AS) ya yi lokacin da ya zama Khalifa, wacce ya rubuta wa Gwamnansa, Malikul Ashtar.
Mahmud Tukur ya ce wannan wasikar za ta iya kawo adalci da kwanciyar hankali a duniya da za a yi aiki da ita.
Littafin na Mahmud Tukur ya shiga duniya sosai. Hatta wasu gwamnatoci a wasu kasashe sun yi amfani da shi.
Sunan littafin da turanci .leadership and governance in Nigeria. By mahmud tukur. Ya shiga sahun littafin da ake sayarwa a duniya ta yanar gizo.
Da Muhammadu Buhari ya shiga siyasa a 2002, Mahmud Tukur yana tare da shi. Shi ne kusan ya jawo masa goyon baya a zaben 2004. A zaben 2011 duk yana tare da shi. Da aka fadi zabe ya ce masa su yi hakuri shekaru da lafiya ba su tare da shi, kamar yadda majiya mai tushe ta tabbatar mani.
Muhammadu Buhari ya amince har ya shelanta ba zai sake takara ba, da aka zo ana neman ya sake tsayawa, Mahmud Tukur ya ce masa kar ya yi, don ana son a yi amfani da shi ne kawai, kamar ya amince. Amma daga baya sai kawai aka ji shi ya yarda ya ci gaba da takara a 2015.
A nan ne Mahmud Tukur ya ce babu ruwansa. Ya yi lissafi da hasashen za a iya cin zaben, amma ya ce yana shakkun za a yi nasarar abin da aka sanya gaba. Don haka ba ruwansa.
Shugaba Buhari ya yi nasara a 2015, amma Mahmud Tukur ya nisanta kansa da gwamnatin. Bai shiga ciki ba, bai taba nema wa kowa komai ba. Bai taba zuwa fadar Shugaban kasa ba. Bai taba halartar duk wani taro na gwamnatin ba. Ba ya kwangila. Ba ya tura kowa a ba shi. Bai taba neman wata alfarma ba, har ya mutu a watan Afrilu na wannan shekarar ta 2021. Shekaru shida da hawan gwamnatin.
An tabbatar wa marubucin nan, Mahmud Tukur ya takaita duk wata huldarsa da Shugaban kasa har ya rasu. Dangantar abokantakarsa da Mamman Daura kawai ya rike. Yakan je gidansa. Sukan kuma yi waya ta zumunci.
Tun da ya ce ba ruwansa, bai tsoma bakinsa ba, har mutuwarsa.
Danjuma Katsina shi ne mawallafin jaridun Katsina City News, Jaridar Taskar Labarai da The Links News.
07043777779.08137777245
Www.katsinacitynews.com
Www.jaridartaskarlabarai.com
Www.thelinksnews.com