Ina neman Ummi Zee-Zee Zan ba bata lakani– Dr. Zahara’u

0

Ina neman Ummi Zee-Zee Zan ba bata lakani– Dr. Zahara’u

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kwamishiniyar mata ta jihar Kano kuma malama mai wa’azi Dr. Zahra’u Muhammad Umar ta ce tana kira ga shahararriyar yar wasan kwaikwayon nan ummi zee zee da aka yada labaran cewa ta ayyana cewa zata kashe kanta da ta zo za ta bata wani lakani,

Dr. Ta ce da ummi zezee za ta ji da sai kawai ta zo ta sameta su rufe kofa domin ta hakurkur dar da ita, domin dai dama duniya ba hutu,

Dr. Dahra’u ta kara da cewa” Abin gaskiya ya dameni kuma ina ganin yar’uwa ta ce mace kuma musulma, ya kamata ni in sameta, ina nemanta ruwa a jallo, Ina neman lambar wayarta, zan gaya mata abubuwan da ya dace ta yi a rayuwarta ubangiji shi ne mai komai, da za mu hadu ido da ido zanji dadi mu zauna da ita.

Indai baa manta ba tun a ranar 3 ga watan Afrilu ne dai ne dai Umme zee-zee ta bayyanawa duniya cewa za ta kashe kanta, saboda damfarar Miliyan 450 da ta ce anyi mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here