Nasara Daga Allah: Mazauna wani kauye a Kankara sun ragargaji barayin daji sama da 30
Yan bindigar kuma sun yi nasarar kashe wani babban mutum a Danmusa
Akalla ’yan fashin daji 30 mazauna garin kauyen Majifa dake karamar Hukumar Kankara jihar Katsina suka lankadawa kashin tsiya bayan sun kawo masu hari a daren jiya.
Mazauna kauyen gami da ’yan sa kai ne suka yi wa ’yan daban dajin kofar rago, lamarin da ya kai ga sun murkushe su farat daya kamar yadda wani mazaunin kauyen ya shaida wa majiyar Katsina Daily Post News, ta Aminiya Daily Trust
An share makonni uku da mazauna ke tunkarar ’yan bindiga a Jihar Katsina.
A Lahadin da ta gabata ce mazauna kauyen Magama da ke Karamar Hukumar Jibia a Jihar suka fafata da maharan kuma suka samu nasarar kashe uku daga cikinsu.
Hakazalika, mazauna kauyukan ‘Yan Marafa da Mununu da ke Karamar Hukumar Faskari ta Jihar, sun yi fito-na-fito da ’yan bindiga, kuma suka yi galaba a kansu.
A wani rahoto mai nasaba da wannan Aminiya ta ruwaito, ’yan bindiga sun kashe wani tsohon Darakta a Ma’aikatar Ilimi ta Karamar Hukumar Danmusa da ke jihar Katsina.
Wannan lamari ya faru ne da misalin karfe 7.30 na Yammacin ranar Laraba yayin da ’yan bindigar suka far wa mutumin a kofar gidansa da ke Danmusa.
“A kan hanyar asibiti ajali ya katse masa hanzari, bayan maharan sun yi kokarin tafiya da shi amma ya tirje, sai kawai suka harbe shi suka tsere,” a cewar wata majiya.
Neman jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sandan Katsina, SP Isah Gambo ya ci tura a yayin da ba iya samunsa ba yayin tattara wannan rahoto.