AN KAI HARI BATSARI TA JAHAR KATSINA

0

AN KAI HARI BATSARI TA JAHAR KATSINA
Daga misbahu batsari
@ jaridar taskar labarai
Da misalin karfe 12:00 na Rana. ta ranar talata 20-04-2021 wasu mahara da ake zargin masu satar dabbobi da garkuwa da mutane ne, suka kai hari kauyukan Hegi da Dan-Alhaji dake karamar hukumar Batsari, jahar katsina.
Sunyi harbe-harbe a garin Dan-Alhaji Kuma sunyi awon gaba da garken awaki. A kauyan Hegi abun baizo da dadi ba, domin bayan sace dabbobi da suka yi, sun harbe wani bawan Allah wanda akayi jana’izar sa da safiyar ranar laraba 21/4/2021. kamar yadda mazauna yankin suka shaida mana.
Karar harbe-harben su ya ruda mutanen garin Batsari,da dama ta yadda, cikin daren hantar jama’a ta kada.
Sannan ko a makon da ya gabata maharan sunkai hari kauyukan Dan-jikko, Salihawar Kalgo da ‘Yan ukku, duk a cikin yankin karamar hukumar Safana .Kuma ansamu asarar rayukan mutum biyar.
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
The links news
Www.thelinksnews.com.
07043777779
08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here