FITACIYYAR YAR JARIDA MURJANATU KATSINA TA RASU
daga kabir Umar Saulawa(PRO)
Allah ya yi ma fitacciyar yar jarida Hajiya Murjanatu Katsina rasuwa da daren jiya Talata 20/4/2021 bayan ta yi fama da rashin lafiya.
Hajiya Murjanatu Katsina tana daya daga cikin maaikatan farko na gidan Radio Tarayya Jamus.
Mai kimanin shekaru 92, marigayiyar kuma ta taba zama Member House of Reps a tsohuwar Gwamnatin Jihar Kaduna.
Za a yi Janaidarta a yau Laraba 21/4/2021 a gidan Marigayi Alhaji Iro Dutsinma Bayan Local Government Secretariat da karfe 10:00 na safe.
Ta rasu ta bar yan Uwa, Dangi da Abokan arziki. Da fatan Allah yayi mata Rahama da Gafara Ameen.