GOBARA A MAJALISAR DOKOKIN KATSINA; WA YA SANYA TA?

0

GOBARA A MAJALISAR DOKOKIN KATSINA; WA YA SANYA TA?

Mu’azu Hassan

@Katsina City News

Gobara ta tashi a Majalisar Dokokin Jihar Katsina a daren Laraba 21/4/2021, yayin da Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari ya yi umurnin a yi bincike don gano me ya haddasa ta.

Binciken farko da jaridunmu suka gudanar, sun gano kamar akwai lauje cikin nadi a faruwa wannan gobarar.

Wani masanin kashe gobara da jaridar nan ta tattauna da shi ya ce, gobarar ta yi kama da wadda ta dade tana ci a cikin babban dakin taron Majalisar a hankali kafin a ankarar, kuma a kashe ta.

Gobara ba ta yi kama da wadda wutar lantarki ta yi sanadin kawo ta ba, domin bincikenmu ya tabbatar mana an fi kwanaki 30 ba a bude wannan dakin taron na Majalisar ba.

Duk wanda ya shiga zai ga alamar datti da kazanta, wadda wutar ta dunkule waje guda. Ma’aikatan Majalisar suna yajin aiki, kuma illahirin Majalisar na kule ba a shiga, balle har kunna wata wutar lantarki.

Bincikenmu ya tabbatar mana a daren da gobarar ta kama, Hukumar ba da wutar lantarki ba ta kawo wuta ba a yankin baki daya har da Majalisar dokokin Jihar. An tabbatar mana da hakan a Hukumar ba da wutar lantarki.

Don haka ba wani karfin hasken wuta da zai iya haddasa gobara a ginin Majalisar, kamar yadda majiyar tamu ta tabbatar mana.

Bincikenmu ya gano maganar yiyuwar karfin wutar lantarki ne ya haddasa gobarar, hujja ce mai raunin gaske.

Ya aka yi wuta ta je har tsakiyar babban ginin na Majalisar? Bincikenmu ya gano wutar ta fi kama da wadda ta rika fantsama a hankali, kamar yadda wani masanin kashe gobara ya tabbatar mana.

Wani abu da ya ba kowa mamaki shi ne, halin ko-in-kula da rashin nuna wata alamar kaduwa da gobarar da ba a gani ba a fuskar ’yan Majalisar.

Wakilanmu sun je ginin Majalisar don wannan binciken sau hudu, amma ba su ga dan Majalisa ko daya ba a harabar ta balle a ji alhini ko takaicinsu na abin da ya faru.

Wakilanmu sun gano hatta lokacin da Gwamnan Katsina ya kai ziyarar jaje da gane wa idonsa abin da ya faru, dan Majalisa daya ya tarbe shi.

A daidai lokacin Kakakin Majalisar yana hanyar sa ta balaguro Abuja, mataimakinsa kuma ba ya gari.

Shi dai wannan babban dakin taro na Majalisar dokokin ba a dade da kashe masa kudi ba aka yi masa gyara na zamani da zama daidai da kowane zauren Majalisa mai kyau a kasa.

Ko a lokacin kwangilar aikin akwai gunaguni a tsakanin ’yan Majalisar, da kuma nune a kan wasu a cikinsu da ake cewa akwai abin tambaya da ba a samu amsarsu ba a kan yadda ake tafiyar da aikin na sake fasalin zauren Majalisar da yanzu ya kone.

Wasu ’yan Majalisar da jaridunmu suka tattauna da su sun ce, lallai suna bukatar a yi binciken mai karfi, kuma mai zaman kansa a kan wannan gobarar ta ginin Majalisar Dokokin Jihar.

Sun ce kamata ya yi a kafa kwamiti mai zaman kansa, kuma na kwararrun masu bincike, wanda za a kaddamar da shi a bayyane, mambobinsa su yi aikin su a bude.

Dan Majalisar ya ce, gaf da Azumi da kuma farkonsa akwai maganganu sosai a tsakanin wasu abokan aikinsa da shugabancin Majalisar, wanda kuma asakalar ta dan yi zafi kafin ta dan kwanta.

Ko mene ne sanadin gobarar? Bincike ne zai tabbatar da wannan.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here