Inna nillah Wa Innailaihiraju’un
A safiyar yau Allah yayiwa Hajiya Maryam Ado Bayero Rasuwa ( Mai Babban daki)
Marigiyiya Hajiya Maryam Mahaifiyar ce ga mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero kuma mahaifiya ga mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero.
Hajiya Maryam ta rasu ne a kasar Masar bayan gajeruwar rashin lafiya.
Anan gaba ne zaa sanar da lokacin yi mata sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Muna Adduar Allah ya gafarta mata.