AN KASHE AWWALUN DAUDAWA.

0

AN KASHE AWWALUN DAUDAWA.
@ jaridar taskar labarai
An kashe babban dan ta addar nan da ya jagoranci satar daliban makarantar sakandare ta Kankara jahar katsina a bara 2020 mai suna awwalun daudawa.
A watanni baya awwalun daudawa ya mika kansa ga gwamnatin zamfara ya shelanta ya tuba kuma yayi Rantsuwa da alkur ani gaban jama a da shelanta cewa in har tada tubar shi al kur ani ya cishi.
A farkon satin nan aka ruwaito awwalun daudawa ya koma daji ya sake daukar makamin shi da tayar da yaran shi don fara sabbin hare hare.
A daren yau aka ruwaito an kashe shi.wasu na cewa wasu daga cikin yan uwansa ne da suka dauke shi Maci amana suka hallaka shi
Wasu kuma na cewa, Rantsuwar sa da Alkur ani ne ta cishi.aka yi nasara akanshi.inda wasu fulanin dake ba gwamnatin zamfara hadin kai suka kashe shi.
Kuma sanarwa da gwamnatin zamfara cewa sun kashe shi.
Jaridar taskar labarai itace ta fara bayyana sunan awwalun daudawa a matsayin Wanda ya ce yaran Kankara. Lokacin da ana ta neman waye ya aikata ta addacin .
Awwalun daudawa yana da alakar safarar makamai da yan boko haram .
Kuma yana kokarin ganin ya kafa sansani iri na jahar naija a tsakanin yankunan zamfara da katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here