A GARIN DAN ALI; AN KWASHE SHINFIDUN LIMAN DAN AYI TSAFI.

0

A GARIN DAN ALI; AN KWASHE SHINFIDUN LIMAN DAN AYI TSAFI.
@ jaridar taskar labarai
A kwanakin baya ne, aka wayi gari a garin Dan Ali ta karamar hukumar dan Musa.aka tashi da wani abin mamaki ,inda aka ga duk shimfidar liman dake massalatan garin an dauke su.
Wani Dan garin da ya tabbatar ma na da faruwar lamarin yace, da farko na Saba samun yan sace sace na shimfidar massalaci Wanda aka dauka aikin barayi ne.
Amma wannan sai aka wayi gari duk masallacin da akaje mashimfidin liman kadai ake dauka.banda na mazaunin mamu.
Wani ya shaida ma jaridun mu cewa shi wannan mashimfidin liman ana hada shi da ruwan wankan gawa a hada wani tsafi na yin nasara akan duk Wanda aka nufa.mutum ko gari.
An zargin barayin daji,wadanda suka matsa ma kauyukan karamar hukumar Dan Musa da sauran yankunan katsina su ake zargi da wannan aika aika.
Wani yace shi wannan tsafi in aka hada shi.har mutum ana iya shigowa gari a sace ba Wanda ya sani.
Wata majiya tace, ana zargin da tsafin aka shiga garin na Dan Ali aka sace wani yaro.har sai da aka biya kudin fansa naira milyan daya aka sako shi.
Ance an shiga har dakin yaron aka dauke shi amma sai da safe aka fahimci an sace shi.
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here