ZUWA GA HADIZA BALA USMAN
@ Danjuma Katsina
Bayan gaisuwa da fatan alheri. Ina jajanta maki abin da ya same ki. Ina kuma tausaya maki rashin adalcin da aka shirya maki.
A Katsina labarin ya fara bayyana ne ta hanyar wani korarren Kantoma, yaro ga Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi. Daga nan yaransa sai suka fara murna kamar wadanda aka yi wa kyautar Hajji da Umara. Sai suka fara yadawa da sharhi marar dadi.
Tarihin Hukumar NPA ba zai cika ba, sai an kawo canje-canjen da kika kawo, wanda ya amfani kasarmu da Afrika baki daya. A hankali wadannan bayanan za su rika fita.
Wannan aikin naki ya ja maki makiya daga manyan ’yan mafiya, wadanda yanzu yaransu ke ta rubutu na bata ki. Karya fure take, ba ta ’ya’ya.
A Katsina kuna da yawa masu rike da mukamai a gwamnatin Tarayya, amma ke kadai ake magana. Wata kalmar hikima na cewa; “Girman ni’imarka, girman hassadarka da makiyanka”.
Kin yi iyakar naki kokarin. A 2019 aka buga wata ’yar mujalla da ta kumshi duk abin da kika yi a Katsina. Ina da kwafi. Kadan daga ciki, kin yi a Kafur, Musawa, Matazu, Mashi, Kurfi, Katsina da sauransu. Kowane da hotuna da bidiyo lokacin da ake aikin.
Fitilu masu hasken rana da kika sanya a makarantun Allo na Jihar Katsina da makabartu duk suna nan ana amfana da su. Kuma almajiran suna maki addu’a daga bakunansu tsarkaka.
Nan gaba kadan karin bayani a kan duk wadannan ayyukan za su fito da kuma tambayar, duk a cikin wadanda suke da mukamai a Katsina, wa zai ja da ke?
Aikinki da yanayin inda kike aikin ya sha bamban da Minista mai cikakken iko. Ko a haka muna sane da yadda kika rika ba da gurbin daukar ma’aikata don a ba ’yan Katsina, amma ana karkatar da su.
Har ’yar kure an taba yi a kan haka. Kin yi niyyar ki gyara, sai wannan jarrabawa ta zo.
Yanzu duniya ta sani cewa, hatta hanyar da aka bi don dakatar da ke, ta kauce wa doka. An yi abin da aka yi cikin gaggawa da niyyar cin zarafi.
Kina da tsare gida, amma kina da tausayi da saukin kai. Kin taimaki mutane da yawa da kudi tsaba a Katsina daga gidan gwamnati zuwa karkara. Don kar a ba ta ladanki da an bayyana, amma Allah ya saka maki da alheri.
Tabbas, kin aikata kura-kurai a matsayinki na ’yar’adam da sauran dalilai, amma a shekarunki, kuskure kamar taki ne da ruwa. Zai kara maki karfin gwiwar fuskantar kalubalen da ke gaba ne, kamar yadda kuma zai kara maki linzami da garkuwa da zamar maki turken mil a gaba.
Shawara ta ta karshe, ki dogara ga Allah, ki kuma dau darasin da ke a cikin wannan jarrabawar.
Za mu sa ido, za kuma mu rubuta a daidai lokacin da ake binciken da ake maganar za a fara.
Wannan ra’ayin na kashin kaina ne, ba na jaridun da nake bugawa a yanar gizo ba.
Jaridar Taskar Labarai. @www.jaridartaskarlabarai.com. Katsina City News @www.katsinacitynews.com. The Links News @www.thelinksnews.com.
Naku
Danjuma Katsina
Marubuci/Dan Jarida.