AN SACE ALKALI A CIKIN KOTU DA RANA TSAKA.

0

AN SACE ALKALI A CIKIN KOTU DA RANA TSAKA.
@ Jaridar taskar labarai
Wasu barayin daji sun je cikin kotun shari ar musulunci, dake garin bauren zakka cikin karamar hukumar safana. Sun tafi da alkalin mai suna Alhaji husaini samaila
Ganau sun shaida ma jaridun taskar labarai cewa karfe uku dai dai alkalin na cikin kotun.maharan suka je.suka harba bindaga sama suka shiga kotun suka tafi da alkalin shi kadai.ba Wanda ya San me ya kai alkalin a kotun ranar kasuwa.ganin ana yajin aiki.kuma kotun ma an chanza mata mazaunin ta saboda tsaro.
Yau talata kasuwar garin ke ci.don haka garin yana cike da yan kasuwa.har zuwa rubuta rahoton nan ba mu samu dalilin tafiya da alkalin ba.kuma babu bayanin ina aka tafi dashi
@ jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here