AN KAI HARI A KANKARA

0

AN KAI HARI A KANKARA
@ jaridar taskar labarai
Mahara sun kai Hari garin majifa karamar hukumar Kankara a daren ranar Alhamis. Sun kashe mutane da yawa.sun jikkatta wadansu duk suna nan asibitin Kankara suna amsar magani .
Maharan sun kuma je makera babba. dake unguwar zango ranar Alhamis sun tafi da mutum daya sun Nemi kudin fansa akan sa ta naira milyan daya.cikin kwanaki uku.in ba a kai kudin ba, zasu harbe shi su kuma kawo Hari a garin.
Masu sa ido ga motsin maharan sun tabbatar cewa, ana ganin su suna taruwa a wani mazauni can nesa da garin.
Wanda a bisa al ada in sunyi irin wannan haduwar zasu kai Hari ne.
Mutanen garin sunyi Kira ga jami an tsaro da su kawo masu daukin kariya kafin maharan su shigo garin.
Mutanen na makera babba, sai barin gari suke suna gudun hijira. Mutanen garin suna ta kwasar kayansu da abinci.suna barin garin .
jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here