KA BIYA TA KUDIN DUKAN TA

0

DAGA DAJIN RUGU
taken labari;
KA BIYA TA KUDIN DUKAN TA….
yankuna da yawa a tsakanin batsari,jibiya,safana da dan Musa.yanzu yan bindiga ke iko.su ake kaima kara.su ke hukunci. Sune kuma hukuma.
Wani mutum diyarsa mai suna Aisha tana aure zaune da kishirya a gidan wani . Sunan kishiyar jummai.( duk mun sakaya sunayen)
Sai Aisha ta kai kara wajen ubanta cewa jummai.ta Kona mata daki.da kaya a ciki saboda zafin kishi.
Uban jummai mai suna hashimu sai ya kai kara wajen shugaban yan bindigar dake yankinsu.
Shugaban yace aje a taho da matar watau jummai..tana isowa aka tambaye ta ke kika Kona dakin Aisha? Tace a a , sai aka samo tsabga akayi ta dukanta har ta suma.
Da ta farfado aka cigaba da duka.
Tana fadin ita bata San komai ba.sai dai a kashe ta.da ta amsa laifin da batayi ba.!
Aka harba bindaga sama aka Dora mata bakin bindigar yana zafi aka ce ta fadi yadda akayi ko a harba.sai kawai ta rika salati da hailala tana fadin a harba kawai.
Don ba ita, tayi ba.kuma ba ta San Wanda yayi ba.bata San ya akayi ba!!!.
Da shugaban yan bindigar yaga duk azaba ya ba matar nan,bata chanza matsayarta ba.
Sai ya wanke ta yace bata da laifi. Sai ya Sanya aka kamo Wanda ya kawo karar, yace masa ka Sanya na zalunci diyar mutane !!.
Don haka hukuncinka.zaka biya matar naira dubu dari da hamsin tayi magani.
Ladar wahalar mu naira dubu hamsin.daukar alhakin da ka Sanya mukayi naira dubu hamsin ko ai maka bulala.dari da tsabgar Geza.
Nan take mutumin yaje ya sayar da wasu shanunsa ya kawo kudin.suka kai wa matar suka ce ta tafi katsina tayi jinya.sauran kudin shugaban yan bindigar ya rike.
Kaji rayuwa a dajin Rugu.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here