YAN BINDIGA SUN KAI HARI WURMA

0

YAN BINDIGA SUN KAI HARI WURMA.
@ jaridar taskar labarai
Wasu yan bindiga sunyi kai Hari da kokarin shiga garin wurma ta karamar hukumar kurfi jahar katsina da yammacin ranar yau laraba 3 ga watan yuni 2021.
Wani dan garin ya shaida ma wakilanmu cewa tun misalin karfe sha biyu na ranar yau aka gan su suna shawagi gefen garin .
Wannan ya Sanya mutanen garin suka dauki matakin shirin kota kwana.da kuma neman daukin jami an tsaro da yan sa kai.
Da misalin uku na yamma ganau sun ce barayin sun taru a wani waje da niyyar fada ma garin.
Cikin taimakon Allah jami an tsaro da hadin gwaiwar yan sakai sun isa garin cikin lokaci.
Majiyar jami an tsaro tace, sun fafata da yan bindigar sun kuma kora su.mutanen garin sun tabbatar mana cewa zuwa jami an tsaro da yan sakai ya taimaka basu shiga garin ba. Anyi bata kashi kuma sun Kore su zuwa cikin daji.
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com.
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here