WAYE GWAMNAN KATSINA A 2023

0

WAYE GWAMNAN KATSINA A 2023

…Nazari daga darasin tarihin baya

Daga Mu’azu Hassan

@ Katsina City News

A shekarar 1992, Shugaban mulkin soja na lokacin, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bullo da wani tsari na mulkin farar hula a Jihohi, mulkin soja a Tarayya. Aka tsara Jihohi su yi zaben Gwamnoni.

A Katsina, manyan ’yan takara biyu suka fito; Alhaji Abu Ibrahim da Magaji Muhammad. Dukkaninsu ga ilmi, iya aiki da kuma sanin manya a sama.

Duk Katsina an dauka cikin su biyu, daya zai fito a jam’iyyar NRC, daya kuma a jam’iyyar SDP, wacce Janar Shehu Musa ’Yar’adua ke bayanta. Kanensa Umaru Musa ’Yar’adua na takara.

Katsina ta dau tsafi kamar yadda yake a tarihi. Kwatsam! Ana gab da zabe, sai Malam Sa’idu Barda yana ma’aikacin gwamnatin Tarayya, ya ajiye aiki ya shigo takara. Babu wanda ya san shi a duniyar siyasa. Ya shiga NRC, kuma shi ne ya zama Gwamna.

A 1999, duk gogaggun ’yan siyasa na Jihar Katsina da kasar nan suna tare da wata kungiya wadda Alhaji Lawal Kaita ke jogaranta, wanda kuma manufarsu a zabi Magaji Muhammad a matsayin Gwamnan Katsina.

Haka aka taho, Umaru Musa ’Yar’adua ya fito takara, amma duk inda za ka gan shi daga shi sai abokansa. Haka aka juya, ana zuwa zaben fitar da gwani Umaru Musa ya yi nasara, kuma shi ne ya zama Gwamnan Katsina na shekaru takwas (Allah ya ji kan sa da rahama).

Umaru Musa na gab da kammala shekarunsa na mulki, kowa ya dauka wanda zai gaje shi, shi ne Kakakin Majalisar lokacin Alhaji Aminu Bello Masari, dan siyasa ne, yana rike da kujera ta hudu a kasa, yana kuma tare da Umaru.

Ana gab da tafiya zaben fitar da dan takara aka yi yawo da sunayen wadanda ya kamata su gaji Umaru. Sam Ibrahim Shema ba ya ciki. A lokacin ba ruwansa da Katsina. Yana can yana bin ofisoshin abokai da wadanda ya sani neman abin da zai rufa wa kansa asiri. Wata majiya ta ce a lokacin har bashi ya fara yi masa tambari, ba shi da kudin zabe, ko shiga takara ko da kuwa ta Dan Majalisar Jiha ne.

Sai aka ce shi ne zai yi takara, kuma ya yi nasara. Sai da ya shekaru takwas yana mulki.

A zaben 2015, ba wanda ya san waye Musa Nashuni, shi ne ya yi takara a jam’iyyar PDP. A taron fitar da gwanin dan takarar APC, Alhaji Aminu Bello Masari ya isa filin taron ba shi da tabbas.

Abokan takararsa sun zo da makudan kudi, mafi yawan deliget nasu ne. Daya daya daga cikin wadanda aka yi taron gabansu cewa ya yi, a zaben fitar da gwanin APC a 2015 babu wani ma tabbacin wa zai kai gaci. Kowa ya iso filin taro ne da dabararsa da kudinsa da fatan shi ne zai yi nasara.

Ya ce deliget ba su da tabbas. Don haka babu mai tabbaci a kan kansa. Allah cikin ikonsa ya ba Alhaji Aminu Bello Masari Gwamnan Katsina.

Irin wannan tarihin haka yake hatta a wasu zabe na fitar da dan takara na zaben Shugaban kasa, misali zaben 1999 da sauran zabubbakan da suka biyo baya a kasar nan.

Tarihi ya nuna duk wanda ya cika zakewa ko ya fara gaba gaba a tarihin siyasar Katsina, ba yakan kai labari ba. Sai dai ya shiga kundin tarihi ya taba nema.

A baya a tarihi, Ambasada Magaji Muhammad ya yi tasiri a neman Gwamna. Bai samu ba har ya bar duniya (Allah ya ji kan sa). Junaidu Mamadu shi ne ya zo na biyu a takarar 1999. Mutane irin su Injiniya Nura Khalil, duk sun yi tasiri. Jadawalin sunayen suna da yawa. Mun kawo biyu ne kawai.

Matasan da wani dan neman takara yake tattatarawa yana wanke masu kwakwale da dora su bisa igiyar zato da tsammani. Ya kamata su rika tambaya masana tarihin baya don shi ne zai zamar masu fitilar haska gaba.

A ra’ayin marubucin nan, mutane biyu sune barazanar da ke fuskantar Jihar Katsina a takarar 2023. Daya wani matashi ne mai kudin gaske a jam’iyyar PDP, dayan kuma wani dattijon ne kuma jibgege a jam’iyyar APC. Allah ka tsare ta daga biyun a zaben 2023.

…Katsina City News

www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

www.jaridartaskarlabarai.com

The Links News

www.thelinksnews.com

07043777779, 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here