ASALIN SARAUTAR SARKIN KUDIN SARKIN KATSINA.

0

ASALIN SARAUTAR SARKIN KUDIN SARKIN KATSINA.
Daga Alhaji Musa gambo k/soro
@ katsina city news
Mutum na farko da aka fara nadawa Sarkin Kudi a gKatsina shi ne Alhaji Abu Kyahi Kofar Sauri, a lokacin mulkin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944).

An haifi Abu Kyahi a shekarar 1870. Asalin zuruyar su mutanen Kukawa ne ta kasar Borno. Kakan Abu Kyahi Malam Ummaru yazo Katsina a shekarar 1820, daga kasar Borno.

Malam Ummaru yazo Katsina tare da matar shi, ya zauna a unguwar Kofar Sauri, Katsina.

A Kofar Sauri Malam Ummaru ya haifi ‘ya’ya masu tarin yawa daga cikin su akwai, Malam Na Maska (1830s-1890s). Malam yayi karatun addinin Musulunci har ya zama babban malami a Kofar Sauri.

Malam Na Maska shi ya haifi Madugu Isah, da Shu’aibu, da Iliyasu da Abu Kyahi.

Daga cikin ‘yayan Malam Ummaru Madugu Isah shi ne babban su, kuma an haife shi wajen karshen shekarar 1840. Ya zama babban dan Kasuwa, kuma jagoran masu fatauci a Kofar Sauri.

Ya shahara wajen cinikin Goro wanda dama ita ce babbar sana’ar zuriyarsu.

Madugu Isah shi ya koya wa Abu Kyahi sana’ar Goro, wanda bayan rasuwar Madugu Isah Alhaji Abu Kyahi ya zama babban dan kasuwar Goro a Katsina.

See also  WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE?

Abu Kyahi mashahurin attajire ne wanda yayi zamani da Sarki Dikko 1906-1944.

Abu Kyahi, rikakken attajiri ne dake zaune a Kofar Sauri. Ya kasance Yana fataucin Goro daga Ankara ta Kasar Ghana zuwa Katsina.

Da aka yi layin Dogo na Railway sai ya rika fataucin goron daga Kurmi zuwa Kano. Daga Kano sai a dauko goron kan Jakuna zuwa garin Katsina.

Saboda karfin arzikin Abu Kyahi har Sarkin Kudi Sarki Dikko ya nada shi. Ance wata shekara da NA ta Katsina ta kasa biyan albashin ma’aikata sai shi Abu Kyahi ya ranta kudi aka biya, sai daga baya aka biya shi.

Kuma shi ne mutum na farko daya fara sayen mota a Katsina baya ga Sarki Dikko.

Har ya zuwa yanzu zuriyarsu Abu Kyahi na nan a Unguwar Kofar Sauri Katsina, daga cikin ‘ya’yan shi akwai

1. Alhaji Danmashi
2. Salisu
3. Bature da sauransu.

Alhaji Musa Gambo Kofar Soro.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here