YAN BINDIGA SUN SACE MUTUNE BAKWAI A JIBIA YAN GIDA DAYA.

0

‘YAN BINDIGA SUN SACE MUTUNE BAKWAI A JIBIA YAN GIDA DAYA.
Daga Ahmad adamu jibia
@ katsina city news

Ranar lahadi 6/6/2021 da misalin karfe 10:30pm na dare wadansu mutane dauke da makamai suka shiga gidan Malam Sa’idu Mai Chemist Jibiya a unguwar gidajen dake like da makarantar day GDSS Jibiya, suka yi awan gaba da shi maigidan da matarsa malama Sa’a da kuma ‘ya’yansu 5, su bakwai ‘yan gida daya.

Sannan sun harbi wani makwabcinsu kurma wanda ya dawo zai shiga gidansu harsashi ya same shi, an garzaya da shi zuwa asibiti. Yana can yana amsar magani

Sun zo ne gab da za’a fara ruwan saman da aka yi da dare wayewar litinin.

Ba wata tirjiya ko wata barazana haka suka korasu cikin daji.

Tun daren lahadi da aka daukesu ba aji duriyar su ba sai ranar talata 8/6/2021 suka bugo wa danshi waya cewa in ana so su bada su sai an basu wasu miliyoyin nairori., yace bai taba ganin su ba balle ya bada sai suka kashe waya.

Ko a kwanaki cikin azumi sun yi awan gaba da masu sallah mutum arba’in a Jibiya.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here