WA ZAI JE AIKIN HAJJIN BANA DAGA KATSINA?

0

WA ZAI JE AIKIN HAJJIN BANA DAGA KATSINA?

Mu’azu Hassan
@ Katsina City News

Yau kwanaki 37 suka rage a yi hawan Arfa, amma har yanzu babu wanda ke da tabbacin mutum nawa za su tafi aikin Hajji daga Nijeriya da kuma Jihar Katsina.

A baya kamar yanzu shiri ya yi nisa, har an saka ranar fara tashi, an kama masaukai a Kasa Mai Tsarki.

A shekarun baya, kamar yanzu babu wajen taruwar jama’a Katsina kamar Hukumar Alhazai.

Maganar gaskiya duk Nijeriya, balle Katsina, babu mai tabbacin ya Hajjin bana zai kasance. Shin za a je? Mutane nawa za su tafi? Ya kuma za a yi tafiyar?

Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina, tana bin duk umurnin da aka ba ta a kan Alhazai, kamar zuwa a tantance su, ko a yi masu allurar kashin farko da ta biyu, ko kuma taron bita. Duk wannan cika aiki ne. Ba tabbacin tafiya ba ne. Don su ma suna cikin duhun me ake a ciki ne.

Kasar Saudiyya, wadda wurare masu tsarki ke cikinta, kuma take kula da tafiyar da aikin Hajji, sako biyu ko uku kawai ta fitar a kan tafiyar aikin Hajjin bana, inda ta ce duk duniya mutane dubu 60 ne kawai za su aikin Hajjin bana.

A baya sama da mutane miliyan biyu ke zuwa aikin Hajji. Yanzu an ce mutum dubu 60.

Ya za a yi kasafin kujerun ga kasashe sama da 150 a duniya? Kasa daya ce ta ce ta yafe, jama’arta ba za su je ba saboda cutar Covid-19, ita ce kasar Indonesia.

A baya ana ba Nijeriya ita kadai kujeru dubu 90, 80, 100, kafin tattalin arziki ya yi zafi, kuma duk su kare.

Har yanzu babu wani shiri da hukumomin Alhazan kasar nan suka yi wa Mahajjata a Kasa Mai Tsarki, don kasar Saudiyya ba ta ba su damar yin hakan ba.

Maganar gaskiya, kuma ta keke-da-keke, babu wani tabbacin aikin Hajji a bana cikin yadda ake tsammani.

Babu tabbacin Jihar Katsina za ta iya samun kujerun da suka kai 200 a cikin dubbai da suka biya kudinsu yanzu suna jiran tsammani cikin shirin ko-ta-kwana.

In an samu kujerun, yadda ma za a raba su shi ne wata maganar babba. Kuri’a za a yi? Ko ya za a yi ta?

Babu wanda ya san wace ka’ida kasar Saudiyya za ta kara bullo da ita da za ta iya shafar Maniyyatanmu.

Zancen gaskiya ana cikin zullumi da yanayin rashin tabbas a kan aikin Hajjin bana.

Tawakalli shi ne kawai makamin duk wani Maniyyaci, kuma ya shirya daukar wa kansa duk sakamakon da ya fito nan da mako daya ko biyu a kan tafiya aikin Hajjin bana daga Nijeriya da kuma Katsina.

Hajji kiran Allah. Wani Hadisi Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Ku je aikin Hajji tun kafin a fara hana ku.”

Kada Allah ya maimaita mana wannan yanayi a kan zuwa Kasa Mai Tsarki don sauke farali.

Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here