RANAR CUTAR SIKILA TA DUNIYA.
TA YAYA ZAMU RAGE YAƊUWAR CUTAR SIKILA?
An ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar yaƙi da cutar amosanin jini wato sikila a faɗin duniya. Rana ce da Majalissar Ɗinkin Duniya ta ware domin faɗakar da al’umma akan wannan cuta ta sikila
Najeriya itace ƙasar da tafi kowace ƙasa yawan masu cutar a duniya. Bincike ya nuna cewa duk shekara ana haifar jarirai 300,000 masu ɗauke da wannan cuta a faɗin duniya, amma rabi daga Najeriya ake haifar su. Daga cikin 150,000 da ake haifa a Najeriya ɗinnan, kusan 100,000 ne suke mutuwa a duk shekara.
Alƙaluman ƙididdiga sun nuna cewa ma fi yawan masu wannan cuta ta sikila da ake haihuwa a Najeriya suna Arewacin ƙasar ne. Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewa rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka rawa sosai wajen haifar yara masu ɗauke da wannan cuta ta sikila a wannan ƙasa tamu Najeriya.
To kamar yanda tun a shekarun baya Gwamnatocin Jihohi da yawa suka tabbatar da dokar yin gwajin cutar ƙanjamau kafin aure, to ya kamata su sake tabbatar da dokar yin gwajin jinsin halitta (GENOTYPE) kafin aure, domin hakan zai daƙile yaɗuwar wannan cuta ta Sikila.
Tabbas akwai ƙarancin ilimantar da al’umma da kuma rashin wayar musu da kai akan sanin amfanin yin gwajin jinsin halitta (GENOTYPE) da rashin sanin ma’anar sa, da kuma sanin muhimmancin yin gwajin tun kafin soyayya tayi nisa har akai ga maganar aure.
To ma’anar GENOTYPE shine; Ƙwayoyin halitta waɗanda Allah (S.W.T) Ya halicci dukkanin mutane tare da wasu, waɗanda suke gudana acikin jiki, wanda waɗannan ƙwayoyin halitta sun kasance tamkar gado ne, ƴaƴa suna samun su ne daga irin nau’in wanda iyayen su suke ɗauke dashi, idan iyaye suka kasance suna ɗauke da nau’i mai kyau, to zasu haifar da ƴaƴa lafiyayyu, idan kuma aka samu akasin haka, to za su haifi ƴaƴa masu rauni wanda zasu kasance suna ɗauke da matsalar amosanin jini wanda ake kira Sikila (Sickle cell anemia).
Idan aka ce mutum yana ɗauke da cutar sikila, ana nufin mutum yana ɗauke ne da sinadaran HAEMOGLOBIN guda biyu marassa kyau a jikin sa, ma’ana waɗanda ba lafiyayyu ba. Cutar Sikila mugun ciwo ne, larura ce da ke raunata duk wani mai fama da ita, har ma da iyalan mai fama da ita, da ma al’umma baki ɗaya.
Masana ilimin kimiyya sun raba GENOTYPE zuwa kaso uku da suke cewa: HOMOZYGOUS DOMINANT, HOMOZYGOUS RECESSIVE, da kuma HETEROZYGOUS.
Mutum zai iya sanin GENOTYPE ɗinsa ne idan anyi masa gwanin jini, wanda idan anyi gwajin ne ake samun ɗaya daga cikin nau’i guda 3 da ake samu kamar haka; akwai AA sune nau’in masu cikakkiyar ƙwayar halitta, ma’ana lafiyayyu kenan. Akwai AS wanda sune nau’in da ake kira da Carrier, wato akwai ɗan rauni a cikin ƙwayar halittarsu, sai kuma na ukun sune SS, ma’ana nau’in masu ɗauke da amosanin jini wato Sikila, saboda raunin ita wannan ƙwayar halittar dake cikin jikinsu yakai maƙura sosai.
Abu mai matuƙar muhimmancin da ya kamata mu fara sani kafin aure shine, mu fara zuwa asibiti domin ayi mana wannan gwaji na GENOTYPE, saboda ta haka ne zamu san wane irin haɗi na aboki ko abokiyar zama zaifi dacewa damu.
Ga yanda rukunin jini yake da kuma yanda masu son yin aure ya kamata su kasance (Rukunin kalmomi na farko na nufin miji, rukunin kalmomi na biyun kuma na nufin mata, sai kuma sakamakon irin ƴaƴan da zasu haifa)
1. AA + AA zasu haifi AA, AA, AA, AA (Idan akayi wannan haɗi a aure za’a samar da ƴaƴa masu cikakkiyar lafiya)
2. AA + AS zasu haifi AA, AS, AA, AS (Shima wannan haɗin aure ne mai kyau kuma babu matsala a lafiyar ƴaƴan da za’a haifa, amma bai kai na rukunin farko ba)
3. AA + SS zasu haifi AS, AS, AS, AS, (Shima wannan haɗin aure ana iya yinsa duk da akwai yar matsala kaɗan akan ƴaƴan da za’a haifa, saboda zasu zama AS ne duka, ma’ana carriers)
4. AS + AS haifi AA, AS, AS, SS, (Akwai matsala a wannan haɗin aure domin za’a samu ɗa ko ƴa mai cutar sikila)
5. AS + SS zasu haifi AS, SS, SS, SS, (Akwai babbar matsala sosai a wannan haɗin aure, domin kusan kaso 80 na ƴaƴan da za’a haifa zasu zama masu cutar sikila)
6. SS + SS zasu haifi SS, SS, SS, SS, (Akwai gagarumar matsala mai muni acikin wannan haɗi na aure, domin dukkanin ƴaƴan da za’a haifa Sikila ne, zasu kasance ne cikin tsanani da wahala na rashin lafiya)
Amma hanya mafi kyau sannan kuma mafi dacewa wajen dakatar da yaduwar wannan ciwo na sikili shi ne idan muka rage auratayya a tsakanin nau’in AS+AS, da AS+SS da SS+SS.
To muna roƙon Allah (S.W.T) Ya ƙara mana lafiya, su kuma ƴan’uwan mu da suke fama da wannan ciwo na Sikili, muna roƙon Allah (S.W.T) Ya cigaba shiga cikin lamarin su, Ya kuma kawo musu sauƙi.
©️ Adamu Kazaure (Ɗan Almajiri)
Email Address: adamukazaure1994@gmail.com