TAKAITACCEN TARIHIN MAKADA ALHAJI MUSA DANKWAIRO MURADUN (1902 – 1991).

0

TAKAITACCEN TARIHIN MAKADA ALHAJI MUSA DANKWAIRO MURADUN (1902 – 1991).

An haifi Makada Alhaji Musa Dankwairo a Shekarar 1902 a Garin Dankadu ayankin Bakura ta Jihar Zamfara.

Mahaifin sa Alhaji Usman Dan Kwanigga ne yabar Kauyensu na Dankadu zuwa Garin Maradun a 1907 lokacin Sarkin Kaya Ibrahim (Sarkin Kaya Iro).

Dankwairo ya samo Sunan Dankwairo ne daga wani Yaron Mahaifin shi, wanda Muryar su tana kama da tashi.

Dankwairo yayi Amshi alokacin Mahaifinshi da kuma Yayan shi Alhaji Abdu Kurna.

Dankwairo ya fara Kidin Noma da Ganga, inda yarikayin Wakokin Noma.

Dankwairo ya fara Waka da Kotso wajajen Shekarun 1950s lokacin Yakin Neman Zaben Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto) a NPC, inda ya fara da wata Waka mai taken –

“Kada Marake Giwa,
Ba’a hayema Barde,
Ahmadu Dan Ibrahimu bai yada Gudun Arna ba”.

See also  DAN KAROTA YA SOKAWA WASU DIREBOBI WUKA A KANO

Dankwairo ya fara Waka ta Kashin Kanshi a Shekarar 1960, bayan an Nada ‘Yandoto Aliyu Sarautar Tsafe. Dankwairo yayi ma ‘Yandoto Wakoki da dama lokacin zamansa a Tsafe.

Bayan rasuwar Yayansa Alhaji Abdu Kurna Maradun, sai Dankwairo ya koma Gida domin Jagiantar Gidan nasu watau a Matsayin Shugaban Tawagar Gidan.

Hakama Dankwairo yayi ma Sarkin Kaya Mai Maradun Wakoki da yawa.

Dankwairo ya karade kusan dukkanin Arewacin Najeriya wajen Waka.

Danjwairo na Gina Wakakokin shine akan Tubulan Ginin Wakar Fada, wadannan Tubula kuwa sun hada da Zambo, Kirari, Yabo, Habaici, Tarihi dadai sauaransu.

Alhaji Musa Dankwairo ya rasu ne a Shekarar 1991. Allah Ya Gafarta tare da sauran Magabatan mu baki daya.

✍️
Aliyu Kassim Yako,
19/06/2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here